1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump zai gana da Xi Jinping na Chaina

Zulaiha Abubakar
June 20, 2019

Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya bayyana cewar zai tabo batun mutanen nan 'yan kasar Kanada wadanda ke tsare a Chaina yayin ganawar da zai yi da shugaba Xi Jinping.

https://p.dw.com/p/3KnMJ
US-Präsident Donald Trump (R) und der chinesische Präsident Xi Jinping in der Großen Halle des Volkes in Peking
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabannin za su tattauna batun zargin kamfanin fasahar sadarwa na Huawei da Amirkan ta yi da leken asiri a taron kasashe masu karfin tattalin arziki da zai gudana a mako mai kamawa. Trump ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Firaiministan Kanada Justus Trudeau a wannan Alhamis.