1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagerun kungiyar Al-Shabaab sun kashe 'yan sanda a Kenya

Zulaiha Abubakar
March 2, 2018

Tsagerun Al-Shabaab dauke da makamai a kasar Kenya sun kashe wa su jami'an 'yan sanda biyar sakamakon wani hari da suka kai yankin gabashin Mandera dake kan iyakar Kenya da Somaliya da asubar yau Juma'a.

https://p.dw.com/p/2taVH
al-Shabaab Kämpfer in Somalia
Hoto: picture alliance / AP Photo

Sanarwar ta kara da cewar Jami'an tsaro na cigaba da bincike a halin yanzu,shi dai wannan hari na zuwa ne kwana daya bayan wasu masu rajin kare hakkin 'dan Adam sun zargi jami'an 'yan sandan kasar da kisan wadanda ake zargi da 'yan kungiyar Al-Shabaab ne da suka dawo daga kasar Somaliya a garin Mombasa.

Kungiyar ta'addanci ta Al-Shabaab na cigaba da kai hare hare gidajen shakatawa da ma'aikatun gwamnati a kasar Somaliya in da kungiyar ta samo asali,mummunan hari na karshe da kungiyar takai a kasar shine wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane sama da 500 a shekarar da ta gabata.