1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsai Ing-Wen ta lashe zaben shugaban kasar Taiwan

Salissou BoukariJanuary 16, 2016

'Yar takarar shugabancin kasa ta bangaran adawa ta lashe zaben kasar Taiwan da aka gudanar a wannan Asabar din da gagarumin rinjaye.

https://p.dw.com/p/1HeeW
Tsai Ing-Wen
Tsai Ing-WenHoto: Reuters/D. Sagolj

Tsai Ing-Wen ta lashe zaben shugaban kasar Taiwan ne da kashi 60 cikin 100, yayin da abokin hamayyarta Eric Chu shi kuma ya samu kashi 30 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada. Sai dai kasar China ta bi sau da kafa wannan zabe, wadda a 'yan watannin baya-bayannan ta yawaita jan kunne ga kasar ta Taiwan ga kaucewa duk wasu babatu na batun samun mulki kai.

Tun dai zaben da aka gudanar na 2008 wanda Ma Ying-Jeou wani na kusa da kasar ta Chaina ya lashe dangantaka tsakanin Chaina da Taiwan ta soma daidaita har ma aka yi ta samun yarjejeniyoyi na harkokin kasuwanci tsakaninsu. Sai dai ana ganin wadda ta lashe zaben na goyon bayan samun incin kan na kasar ta Taiwan.