1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana yin zafi mai tsanani a Turai

Abdourahamane Hassane
June 25, 2019

Ana yin tsananin zafin rana a kasashe da dama na nahiyar Turai, wanda kuma zai ci gaba da karuwa a tsawon mako.

https://p.dw.com/p/3L4NK
Frankreich | Hitzewelle
Hoto: Getty Images/AFP/C. Archambault

A Faransa inda a yau a wasu sasan kasar matsayin zafin ya kai maki 35 a ma'aunin Celicius, kwarraru sun ce zai haura da maki 41 a cikin makon. Masu yin hasashe a kan yanayi sun ce a tsakiyar wannan mako a Jamus za a yi tsananin zafin ranar  da ba a taba yin irinsa ba a cikin shekaru 70. Yayin da a kasashen  Beljiyam da Spain da Ostiriya  can ma zafin ranar zai haura.