1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanonin inshora na daukar nauyin marasa lafiya

February 14, 2020

Shirin Lafiya Jari na wannan mako ya duba tsarin inshorar lafiya a Jamus yadda ya zama dole ga duk wanda ke zaune a kasar ya yi rijista da kamfanin inshorar lafiya.

https://p.dw.com/p/3XmQt
Symbolbild - Arztbesuch - Blutdruck
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Klose

A tarayyar Jamus a bisa doka dole ne duk mazaunin kasar ya yi rijista da kamfanin inshorar lafiya. Kama daga ma’aikata da kananan yara da matan aure da marasa aikin yi hatta ‘yan gudun hijira tilas ne hukuma ko ma’aikatar da mutum ke aiki ta yi masa rijistar inshorar lafiya. Frau Dr Heidrun Hübner wata likita ce da ta kwashe shekaru 20 tana aiki. Ta ce:'' Kananan yara na cin gajiyar inshorar lafiya ta iyayensu. A nan kowa yana biyan kudin inshorar lafiya a duk wata. A don haka da mutum ya zo wurin mu zai samu kulawa kuma za mu ba shi magani. Idan mutum yana da inshora  to zai iya zuwa mana nan da kowace irin rashin lafiya, mu kuma za mu ba shi magani wanda kamfanin inshorar lafiya zai biya mu kudin daga baya.

Jama'a a Jamus na tafe da katin inshorar lafiya saboda kula da kiwon lafiyarsu

Symbolbild - Gesundheitskarte
Hoto: J. Kalaene/dpa/picture-alliance

A nan Jamus dai mara lafiya ba ya tafiya asibiti kai tsaye, sai ya fara zuwa gidan likita, likitoci na duba lafiyar mutum ne su kuma bayar da shawara. Idan suka fahimci mara lafiya na bukatar kwanciya a asibiti nan take suke tura mutum ba tare da ba ta lokaci ba. To amma abu na farko da mara lafiya ke fara nunawa a gidan likita, shi ne katin shaidar cewa yana da inshorar lafiya. Alicia Smith ‘yar kasar Canada ce da ke aure a birnin Bonn. Ta ce:''Na kan ajiye katin inshorata a ‘yar jakar da nake rikewa kowane lokaci, na kan yi haka ko da zan bukaceshi. Amma na san cewa idan alal misali na yi hadari a kan hanya kuma ana son yi min aiki a asibiti ba sai an sha wahalar neman bayanai na ba, domin idan har na samu hadari ba zan iya komawa gida in nemo katin ba.''  Yayin da Zipporah ke ganin akwai bukatar gwamnatocin Afirka su tilasta wa jama’a yin inshorar lafiya kamar yadda ake yi  a nan Jamus domin maganin matsalolin kiwon lafiya, Umaru Aliyu na ganin akwai bukatar a fara magance talauci wanda idan har da shi a tsakanin jama'a to tunanin mutane yana kan abin da za su kai bakinsu ba wai inshorar lafiya ba.