1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaro a Najeriya da Nijar cikin mummunar hali

Abdourahamane Hassane
September 2, 2021

A yayin da a Najeriya ake ci gaba da ba da rahotannin sace-sacen 'yan makaranta tare da yin garkuwa da su a yankin arewa maso gabashin kasar. A Nijar a yammacin kasar hukumomin ne suka dage dokar haramta hawan babura.

https://p.dw.com/p/3zp3u
Nigeria Soldaten patrouillieren in Tungushe
Hoto: AFP/Str

Al'amura na kara yin muni a arewa maso gabashin Najeriya, inda ake ci gaba da sace dalibai tare da yin garkuwa da su a sassa dabam-dabam na yankin arewacin,Abin da ya tilasta wa shugabanin a Jihar Zamfara zartas da dokar rufe kasuwanni da makarantu tare da haramta sayar da man fetir da dai sauran mataka.Yayin da a Nijar a yankin yammacin a Jihar Tillaberi duk da irin yada ake kai hare-hare a jihar hukumomi suka dage dokar haramta hawan babura. Daga kasa mun tanadar muku da rahotanni dangane da wannan batu