1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsawaita dokar ta baci a wasu jihohin arewacin Najeriya

November 7, 2013

Majalisar dattawan Najeriya ta ce tilas ne shugabannin rundunonin tsaron kasar su bayyana a gabanta dangane da batun dokar ta baci.

https://p.dw.com/p/1ADsg
Nigerian soldiers patrol in the north of Borno state close to a Islamist extremist group Boko Haram former camp on June 5, 2013 near Maiduguri. Nigeria's military yesterday disclosed details of its offensive against Islamist militants, describing a series of events that saw insurgents take control of a remote area before being pushed out by soldiers. AFP PHOTO / Quentin Leboucher (Photo credit should read Quentin Leboucher/AFP/Getty Images)
Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

Kasa da awoyi 24 da ayyana bukatar neman karin wa'adi na watani shida, 'yan majalisar dattawan Najeriya sun amince da tsawaita dokar ta baci a jihohin Borno da Yobe da ma Adamawa.

Babu dai bata lokaci balle batu na jan kafa a bangaren 'yan majalisar dattawan Najeriya, da suka zauna suka ce sun kai ga amincewa da bukatar da shugaban kasar ya gabatar, ta neman karin wa'adi na watani shida, da nufin kawo karshen rikicin da ya tada hankula dama asara na rayuka.

Ra'ayi dai yazo daya a tsakanin masu adawa dama 'ya'yan jam'iyyar PDP mai mulki, wajen amincewa da sabuwar bukatar da ke nufin daukacin jihohin Yobe da Borno da ma Adamawa za su ci gaba da kasancewa karkashin iko na tsaron soja, har na tsawon wasu kari na watanni shida masu zuwa.

Description en:House of Representatives of Nigeria Date 16 September 2005, 11:13 Source The House of Representatives Author Shiraz Chakera ou are free: to share – to copy, distribute and transmit the work to remix – to adapt the work Under the following conditions: attribution – You must attribute the work in the manner specified by the author or licensor (but not in any way that suggests that they endorse you or your use of the work). share alike – If you alter, transform, or build upon this work, you may distribute the resulting work only under the same or similar license to this one.
Ginin majalisar dokokin NajeriyaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Adawa da tsawaita dokar ta baci

To sai dai kuma daga dukkan alamu har ya zuwa yanzu kai yana rabe a tsakanin sassa daban daban na dattawan da ke wakiltar yankin, game da makomar rikicin dama mafitarsa ga dubban daruruwan al'ummar da yanzu haka ke rayuwa ta Allah sarki.

Senator Ahmed Zanna dai na zaman dan majalisar dattawan kasar da ke PDP, da kuma ke kallon saka dokar ta bacin, da tura sojan na zaman babban kuskure ga gwamnatin da a cewarsa ke nuna alamar rudewa kan matsayin da yankin ke ciki a yanzu.

Tsawaita sabuwar dokar dai na ci gaba da fuskantar jeri na adawa daga sassa daban daban da suka hada har da gwamnatin jihar Adamawa da ta kirashi daura yaki bisa al'umarta. Ana dai zargin karin gishiri a cikin raunin da ya galabaitar da al'ummar jihohin uku, da suka share tsawon watanni shida na farkon dokar cikin matsi da halin kunci, sannan kuma suke shirin fara wasu sababbi na shidan a cikin yanayi maras tabbas.

Autor: Ubale Musa (Korr DW).in Abuja, Nigeria Below are  the pictures of the arrival of the security meeting  PIC FROM LEFT: CHIEF OF DEFENCE STAFF, ADMIRAL OLA IBRAHIM; CHIEF OF ARMY STAFF, LT.-GEN AZUBUIKE IHEJIRIKA AND  CHIEF OF DEFENCE INTELLIGENCE, MAJOR-GEN. SANI AUDU ARRIVING FOR A MEETING AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON THURSDAY (4/3/13)
Shugabannin rundunonin tsaron NajeriyaHoto: DW

Goyon baya tare da aza ayar tambaya

To sai dai kuma a fadar Senato Maina Ma'aji Lawal, da ke zaman dan majalisar dattawan na jihar Borno karkashin jami'iyar adawa ta APC, ci gaban dokar na zaman wajibi duk da jerin matsalolin da ta haifar.

Kokarin shawo kai ko kuma kokari na kara yin adawa dai, duk da amincewar 'yan majalisar na tsawaita lokacin dai, dattawan kuma sunce za su nemi tozali da shugabanni na rundunonin tsaron da ke jagorantar yakin, da nufin neman amsa jeri na tambayoyin da ke da daure kai.

Tambayoyin kuma da a cewar Senator Ali Ndume za su taimakawa kokarin rarrabe aya cikin tsakuwar da yanzu haka ke barazana ga tuwon daukacin al'ummar ta arewa maso gabas.

Amsoshin kuma da kila ke iya haskaka hanya ta gaba, a tsakanin al'ummar kasa da ke yi wa rikicin kallon matsala ta siyasa da zamantakewa dama kokari na gurguncewar daukacin al'ummar yankin.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani