1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsige gwamnan Jihar Adamawa ya zama koma baya ga 'yan adawa

July 15, 2014

A Tarayyar Najeriya Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako ya zama dan jam'iyyar adawa ta APC na biyu da ya rasa mukamunsa cikin lokaci kadan

https://p.dw.com/p/1Cde6
Murtala Nyako
Hoto: DW/U. Shehu

A wani matakin da ke zaman sabon salo na siyasar Tarayyar Najeriya gwamnonin APC na jam'iyya adawa na ci gaba da rasa madafun iko.

An dai fara ne tare da kai karshen mulkin APC a Jihar Ekiti a wani abin da jam'iyyar ta kira magudi mafi tada hankali na lokaci mai tsawo kafin daga baya a gangara zuwa Adamawa inda 'yan majalisar jihar suka tsara kada kuri'a bisa makomar gwamnan jihar Murtala Hamman Yero Nyako da majalisar jihar ta zarga da cin amanar al'umar jihar, inda daga baya kuma guguwar ta koma Jihar Nasarawa a can ma dan uwansa Tanko Almakura ya fuskanci tasa barazanar a wani abun da ke zaman kokari na karya adawa daga Abuja wadda ke shirin fuskantar zabe a cikin hali na rashin tabbas.

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria Fernsehansprache ARCHIV
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

'Yan adawa suna zargin gwamnatin kasar karkashin Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP da neman kawar da wasu gwamnoni kafin zaben 2015. Gwamnonin da suka hada da Ekiti, da Osun da Edo da Adamawa da Nasarawa da kuma Borno. Shugaban kasar da ya share lokaci mai tsawo yana ganawa da gwamnonin jam'iyyarsa ta PDP da nufin shaida masu burinsa na takara a zabukan da ke tafe.

Ficewar 'yan biyar na gwamnonin PDP ya zuwa APC dai ya kai ga barazana mafi girma a shekaru 15 na mulkin jam'iyyar. Abun jira a gani dai na zaman mafita a cikin sabuwar takaddamar da ke iya kai wa ga sauyi na siyasa dama kila tasirinta ga tsarin demokaradiyar da ke tangal-tangal ya zuwa yanzu.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Suleiman Babayo