1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsipras da EU na nazari kan bashin Girka

Mouhamadou Awal BalarabeJune 24, 2015

A daidai lokacin da ministocin kudi na kasashen EU suka gudanar da taron gaggawa kan matsalar bashin Girka, kawunan 'yan kasar ya rabu kan matakan tsuke bakin aljuhu.

https://p.dw.com/p/1Fmw9
EU Griechenland Tsipras mit Juncker
Hoto: Reuters/J. Warnand

Wannan dai shi ne karo na biyu da firaministan Girka Alexis Tsipras ya nika gari i zuwa cibiyar EU a cikin wannan makon, don ganawa da bangarorin da ke bin kasarsa makudan kudade. Dalili kuwa shi ne mako guda ya rage kasarsa ta fada cikin talauci idan bai yi nasarar mangance rikicin kudin da ya addabi Girka ba. Hasali ma dai batu daya tilo ne ya ke daukar hankalin ministocin EU da sauran manyan jami'ai na IMF da babban bankin Turai, wanda ba wani ba ne illa nazarin matakan tsuke bakin aljuhu da Girka ta yi alkawarin dauka, kafin daga bisani a yanke shawarar fitar da ita cikin kangin da ta shiga koko a'a.

Ita dai gwamnatin Alexis Tsipras ta sha alwanshin kaddamar da sauye-sauyen tattalin arziki domin tattalin arzikinta ya samu ya bunkasa, tare da samun kudin da za ta biya bashin da ya zo mata iya wuya. Saboda haka ne gwamnatin ta Athenes ta ce za ta kara haraji tare da yi ma tsarin pensho gyaran fuska. Lamarin da zai bawa Girka damar samun biliyan bakwai da 200 da ta ke bukata daga takwarorinta na Turai domin biyan IMF kaso na bashi da ta saba biya.

Euro-Skulptur in Frankfurt am Main Symbolbild
Kasashen da ke amfani da Euro ne ke taimaka Girka biyan bashintaHoto: picture-alliance/dpa/D. Reinhardt

Ministan kudin kasar Faransa Michel Sapin ya yi tsaokaci kan bashin da ake bin kasar ta Girka, inda ya ce "Ba wai jami'an bankuna ne ke bin 'yan Girka bashi ba. Gaba dayan kasashen da ke amfani da Euro ne ke binsu bashi kama daga 'yan Faransa da Jamus da Italiya da Spain da sauransu. Kasancewa batu ne da ya shafi kasashe da dama, saboda haka ne ya zama wajibi kasashe su hada gwywa don samar da maslaha."

Sai dai kuma babbar matsalar da firaminista Alexis Tsipras zai fuskanta ita ce adawa ta cikin gida. Idan dai za a iya tunawa alkawarin da ya yi na yin watsi da matakan tsuke bakin aljuhune suka bashi damar lashe zabe tare da zama firaminista. Saboda haka ne ake ganin cewar zai fuskanci turjiya daga majalisa kafin ta amince da kudoririn da zai mika mata domin albarkanta kan nan da mako guda.

Wasu daga cikin 'yan Girka dai na ganin cewar dole firaministansu ya bada kai domin bori ya hau, saboda ita ce hanya daya tilo ta magance kanfar aljuhu da suke fuskanta. Yayin da wani bangare na al'umma kuma ke ganin cewar firaminista Tsipras ya sabawa manufofin gwamnatinsa na juya baya ga duk matakan tsuke bakin aljuhu.

Amma kuma wasu daga cikin jam'iyyun kasar ta Girka na goyon bayan firimiya Tsipras, inda ta kai shugaban jam'iyyar da ke da tsaka-tsakin ra'ayin, Stravos Theodorakis ya je Bruxelles don ganin cewa hakar Girka ta cimma ruwa. A lokacin da aka tambayasa abin da ya yi a cibiyar ta EU, ya ce "Na gana da komishinan Eu da ke kula da harkokin kudi da tattalin arziki Pierre Moscovici. Sannan kuma zan gana da komishinan da ke kula da zuba jari da kodago, da ma dai sauran shugabannin Turai , don ganin an hanzarta shawo kan matsalar da ake ciki."

Griechenland Kundgebung linker Organisationen
Majalisar Girka za ta zamewa Tsipras kalubale a rikicin bashiHoto: DW/P. Kouparanis

A ranar Alhamis da Jumma'a ne za ta ware ko kuma ta warware ma Girka a taron da shugabannin kasashe da gwamnatoci na Turai za su gudanar a Bruxelles don cimma matsaya kan matsalar ta Girka.