1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsit na minti guda bayan hare-haren ta'addancin birnin Paris

Mohammad Nasiru AwalNovember 16, 2015

A kasashen Turai baki daya an yi shiru don juyayin wadanda hare-haren ta'addancin ranar Jumma'a da dare a birnin Paris suka rutsa da su.

https://p.dw.com/p/1H6b0
Frankreich Schweigeminute nach Terroranschlägen in Paris
Hoto: Getty Images/AFP/S. de Sakutin

Da karfe 12 ranar wannan Litinin kasar Faransa da sauran kasashen Turai sun yi shiru na tsawon minti guda don tunawa da wadanda hare-haren ta'addanci mafi muni da ya auku a birnin Paris suka rutsa da su. A Paris shugaba Francois Hollande da wakilan majalisar ministocinsa da daruruwan mutane sun hallara a dandalin Place de la Republique da ke kusa da daya daga cikin wuraren da aka kai hare-haren na ranar Jumma'a da suka halaka akalla mutane 129, inda suka tsit na minti guda.

A can kasar Turkiyya ma shugabannin kasashen kungiyar G-20 da ke halartar wani taron koli sun bi sahun sauran kasasahen Turai wajen yin tsit na minti daya don alhini ga wadanda hare-haren na Paris suka rutsa da su. Mahalarta taron sun sha alwashin kara kaimi wajen yaki da ta'addanci a duniya. Mai masaukin baki shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan cewa yayi.

"Ta'addanci na zama barazana garemu duka baki daya. Ya shafi zaman lafiyarmu da kuma tsaronmu."

Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel karawa ta yi da cewa.

"A gun wannan taro na G-20 muna aikewa da wani sako mai karfi cewa kanmu a hade yake kuma mun fi duk wani aikin ta'addanci karfi."