1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsofon ministan taimakon raya kasa na Jamus ya gabatar da littafinsa

June 22, 2005

A yau laraba ne tsofon ministan taimakon raya kasashe masu tasowa na Jamus Gerhard Eppler ya gabatar da littafinsa dake sukan lamirin manufofin taimakon raya kasashe masu tasowa na kasashen yammaci

https://p.dw.com/p/BvbA
Bangon littafin Eppler
Bangon littafin Eppler

Ko da yake Gerhard Eppler ya samu shekaru 78 da haifuwa kuma furfura ta dabaibaye kansa, amma in banda hakan ba a hangi wata alamar rauni tattare da shi ba a lokacin da ya dare kann mimbari domin gabatar da jawabi akan littafinsa dangane da manufofin gwamnati da ya ce sun zama tsofon yayi. Epppler ya rike mukamin ministan taimakon raya kasashe masu tasowa na Jamus daga shekarar 1968 zuwa ta 1974. Ya ce maganar taimakon raya kasa ta dade tana ci masa tuwo a kwarya, musamman ma a yanzu, inda ake dada mayar da nahiyar Afurka ‚yar rakiya a kusantar juna da ake samu a fannin tattalin arziki tsakanin sassan duniya dabam-dabam. Eppler ya kara da cewar:

2. O-Ton Eppler

„A cikin shekaru 20 da suka wuce an dada samun karuwar gibi tsakanin kasashe matalauta da kasashe masu wadatar arziki, lamarin da ya kai aka yi ko oho da wata nahiya gaba dayanta. Nahiyar Afurka ba ta da sauran auki illa kawai cin moriyar albarkatun mai da sauran albarkatun da Allah ya fuwace mata.“

Eppler ya ce ko shakka babu akwai wasu ‚yan tsirarun kasashen dake cin gajiyar wannan kusantar junan da ake samu sakamakon ci gaban tattalin arzikin da suke samu, kamar dai ATK da Botswana da Uganda da Namibiya, amma a hakika kasashe matalauta ‚yan rakiya ne kawai a wannan manufa. Kasashen Afurka dake kudu da hamadar sahara ba su taka wata rawa ta a zo a gani a dangantakar tattalin arziki ta kasa da kasa. Duka-duka kasonsu a harkokin ciniki na duniya bai zarce kashi biyu cikin dari ba. Tsofon jami’in siyasar na SPD sai ya kara da cewar:

4. O-Ton Eppler:

„Yawan kudaden jari da kamfanonin Jamus ke zubawa a nahiyar Afurka bai kai kashi daya cikin dari ba daga yawan kudaden da suke zubawa a kasashen ketare. Nahiyar ga alamu ba ta da wani muhimmanci a idanunsu.“

Bisa ga ra’ayin Eppler yaduwar salula a kasashen Afurka ba ya ma’anar ana damawa da nahiyar a harkokin ciniki na duniya. Domin kuwa birnin Tokyo na kasar Japan kadai na da layukan tarfo da yawansu ya zarce na nahiyar Afurka baki dayanta. Daya matsalar kuma ita ce ta mummunar barazanar da ake fuskanta a game da wargajewar wasu kasashen na Afurka. Misali kasar Kongo inda a halin yanzu haka kungiyoyi na ‚yan ta-kife ke cin karensu babu babbaka. Irin wannan ci gaba shi ne ke hana ruwa gudu wajen raya makomar kasashe da dama dake tasowa. A duk inda ba a da wata tsayayyar gwamnati to kuwa da wuya kasa ta samu ci gaba, musamman a fannin tattalin arziki, kamar yadda ake gani yanzu haka a kasashe irinsu Somaliya da Kongo da Liberiya da makamantansu. Nahiyar Afurka na bukatar taimako da kyakkyawan hadin kai daga sauran kasashe domin raya makomarta da kuma samun wata kafa ta cin gajiyar kusantar tattalin arzikin da ake samu tsakanin kasa da kasa in ji tsofon ministan taimakon raya kasashe masu tasowan na Jamus Gerhard Eppler.