1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gbagbo ya kafa sabuwar jam'iyyar siyasa a Côte d'Ivoire

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
October 18, 2021

Tsohon shugaban Côte d' Ivoire Laurent Gbagbo ya dasa dambar komawa fagen siyasa, inda bayan kusan shekaru 10 yana tsare a gidan yarin ICC, ya kaddamar da sabuwar jam'iyyar siyasa mai matsakaicin ra'ayin gurguzu.

https://p.dw.com/p/41pfv
Elfenbeinküste | Rückkehr von Ex-Präsident Laurent Gbagbo
Hoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Wakilai 1,600 sanye da riguna da kuma mayafai da ke dauke da hoton tsohon shugaban Côte d' Ivoire ne suka halarci babban taron da ya gudana a birnin Abidjan. Sun shafe tsawon kwanaki biyu suna shawarwari kan ginshikin da ya kamata su dora sabuwar jam'iyyar Laurent Gbagbo a kai. Amma a karshe sun amince  jam'iyyar «PPA-CI» Parti des Peuples Africains-Côte d'Ivoire ta zama ta gwagwarmayar hada kan nahiyar Afirka, bai dai domin ta fara magana da murya daya nan gaba, kamar yadda Issa Malika Koulibaly, daya daga cikin kusoshin jam'yyar ya bayyana.

Karin bayani: Ganawar Alassane Ouattara da Laurent Gbagbo

"Bambancin zai kasance a fannin manufa. Sabuwar jam'iyyar za ta kasance jam'iyya mai maraba da kowa. Za ta kasance ta hada kan Afrika. Don haka sabanin jam'iyyar FPI, za ta kasance ta duk wanda ya amince da matsakaicin ra'ayin siyasar gurguzu a nahiyar Afirka da kuma kasar Côte d' Ivoire. Sannan kofofinta za su kasance a bude ga sauran jam'iyyun siyasa masu matsakaicin ra'ayin gurguzu a Afirka saboda Shugaba Laurent Gbagbo yana dora wannan sabuwar jam'iyyar a kan mizanin Afirka."

Magoya bayan Laurent Gbagbo suna yi masa maraba a lokacin da ya koma gida
Magoya bayan Laurent Gbagbo suna yi masa maraba a lokacin da ya koma gidaHoto: Luc Gnago/REUTERS

Laurent Gbagbo da abokansa sun kirkiri wannan sabon tsarin siyasa ne da zummar samun angizo a nahiyar Afirka ta hanyar kafa reshen PPA-CI a kowace kasa. Wannan tsarin dai ba sabon abu ba ne a kasashen rainon Faransa. Ko da a shekarar 1946, an samu jam'iyyar da ta yi irin wannan gagwarmaya. Don Mello da ke da kusanci da Laurent Gbagbo ya ce ta wannan hanya ce kawai za a hada karfi da karfe don tsamo Afirka daga mawuyacin hali da take ciki.

Karin bayani: Laurent Gbagbo ya koma gida

"Kamar yadda aka samar da jam'iyyar RDA don share fagen neman 'yancin kai, mun kafa wannan don samun ingantaccen 'yancin kai."

Simone Gbagbo tsohuwar matar Laurent Gbagbo, ba ta halarci bikin kaddamar da sabuwar jam'iyyarsa ba
Simone Gbagbo tsohuwar matar Laurent Gbagbo, ba ta halarci bikin kaddamar da sabuwar jam'iyyarsa baHoto: Julien Adayé/DW

Sai dai Simone Gbagbo, tsohuwar abokiyar gwagwarmaya kuma tsohuwar mai dakin Laurent Gbagbo ba ta halarci bikin kaddamar da jam'iyyar PPA-CI ba. Amma magoya bayan Gbagbosun fito daga ko ina cikin Côte d' Ivoire don shaidar da wannan babban taron, kamar Nicolas Kla.

"Na shafe fiye da kilomita 500 daga San Pedro don zuwa nan Abidjan. Amma mun halarta ne don nuna cewa mu 'ya'yan jam'iyyar ne na hakika, don nuna cewa mun yi fafutuka wajen ganin an kafa wannan sabuwar jam'iyya. Wannan wata sabuwar madogara ce ta gwagwarmayar sake karbar ikon gwamnati a nan Côte d'Ivoire."

Kirkirar jam'iyyar PPA -CI da Laurent Gbagbo ya yi, ya ba shi damar juya shafin tsohon tsarin siyasarsa ta jam'iyyar FPI. Daga cikin abubuwan da suka ba da sha'awa a wannan babban taron, har da wakilci da aka samu daga wasu jam'iyyun kamar PDCI-RDA ta tsohon Shugaba Henri Konan Bédié da RHDP ta Shugaba Alassane Ouattara, lamarin da ke zama wata alama ta hadin kan kasa da ta fara samuwa bayan rikicin siyasa na 2011 a kasar ta Côte d' Ivoire.