1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta gurfanar da tsohon shugaban Kataloniya

March 25, 2018

Tsohon shugaban yankin Kataloniya na Spain Carles Puigdemont zai gurfana a gaban kotun Jamus ranar Litinin.

https://p.dw.com/p/2ux7B
Carles Puigdemont
Hoto: Imago/Agencia EFE/A. Dalmaux

Tsohon shugaban yankin Kataloniya na kasar Spain, Carles Puigdemont da hukumomin Jamsu suka cafke zai gurfana a gaban kotu a wannan Litinin mai zuwa. An kama Puigdemont sakamakaon sammaci na kasa da kasa da Spain ta bayar bisa tuhumansa da laifukan tayar da tawaye.

'Yan sandan Jamus sun kama Carles Puigdemont lokacin da yake yunkurin shiga kasar daga kasar Denmak.