1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun yi tsokaci kan nahiyar Afirka

Salissou Boukari
August 20, 2018

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi tsokaci kan ganawar da aka yi tsakanin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaba Issoufou Mahamadou na Nijar a ziyarar da ya kawo a birnin Berlin.

https://p.dw.com/p/33Pen
Deutschland Merkel trifft Mahamadou
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Hirschberger

Jaridar ta ce an kuduri aniyar daidaita al'amura a Nijar. Ta ce shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi wa babban bakon nata alkawarin karin taimako daga Jamus da kungiyar Tarayyar Turai don tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel da kula da 'yan gudun hijira da kuma wani tallafin samar da ababan more rayuwa a Nijar. Jaridar ta karo na hudu ke nan cikin shekaru biyar da Merkel ta gana da shugaban na Nijar, kasar da ke da matukar muhimmanci a kokarin dakile kwararar bakin haure zuwa Turai da kuma yaki da masu ikirarin jihadi a yankin Sahel. Nijar na a jerin kasashe biyar da suka hada da Mali da Burkina Faso da Mauritaniya da Chadi da suka samar da rundunar sojoji kimanin 5000 da ake kira G5 Sahel.

Shugaba IBK ya lashe zaben Mali

Mali Wahlen - Ibrahim Boubacar Keita
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita zai ci gaba da rike madafun iko inji jaridar Die Tageszeitung a labarin da ta buga game da zabe zagaye na biyu da aka gudanar a kasar Mali, mai fama da rikicin 'yan tarzoma.

Jarida ta ce kamar yadda aka yi hasashe, yanzu dai ya tabbata cewa Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da ake wa lakabi da IBK, zai yi sabon wa'adi na biyu bayan ya yi nasarar lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Mali da aka gudanar a ranar Lahadi. Shugaban dai ya kada abokin takararsa kuma jagoran 'yan adawa Soumaila Cisse, wanda ya yi zargi an tabka magudin zabe. Sai dai masu sa ido a zabe na kungiyar Tarayyar Turai sun ce ko da yake an tabka kurakurai masu yawa a zaben, amma ba su shaida wani aringizon kuri'u ba. Yanzu dai IBK wanda a wa'adin farko na shugabancinsa bai tabuka wani abin kirki na magance matsalar tsaro a kasar ba, ana fata a wannan karon zai ba wa marada kunya.

Rikicin cikin gida na damun kasar ta Habasha

Abiy Ahmed Äthiopien
Hoto: Reuters/T. Negeri

Jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan makon ta leka kasar Habasha ne tana mai cewa matashi shugaban kasar Habasha na fama da kalubale a sassa daban-daban, sannan sai ta ci gaba kamar haka:

Ta ce shugaban kasa Abiy Ahmed na shan yabo dangane da sulhun da ya yi da makwabciyar kasa Eritriya, amma a cikin gida yana fama da tashe-tashen hankula na yankuna. A kwanakin nan an kashe wasu malaman cocin Orthodox su shida sannan aka kone majami'u takwas a wani rikici da ya auku a gabashin Habasha. Rahotanni sun ce gwagwarmayar neman rike madafun iko tsakanin hukumomin yankin da gwamnatin tsakiya karkashin sabon Shugaba Abiy Ahmed ne musabbabin rikicin. Yanzu kalubalen da ke gaban shugaban shi ne yadda zai shawo kan irin wadannan rigingimu da ake samu nan da can a kasar ta Habasha.

A karshe sai kasar Yuganda inda a labarin da ta buga jaridar Die Tageszeitung ta ce matashi mawakin nan da ya rikide ya koma fagen siyasa da ake wa lakabi da Bobi Wine ya zargi 'yan sanda da harbe masa direba har lahira lokacin wani yakin neman zabe a arewa maso yammacin kasar ta Yuganda. Hakan ta faru ne bayan yakin neman zaben da Shugaba Yoweri Museveni ya gudanar a yankin. 'Yan sanda sun cafke matashin dan siyasa da ya yi suna wajen sukar lamirin Shugaba Museveni.