1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsokacin Paparoma kan sauyin yanayi a duniya

Zainab Mohamed AbubakarNovember 27, 2015

Paparoma Francis ya kalubalanci shugabannin kasashen duniya da su cimma sahihiyar yarjejeniya na yaki da sauyin yanayi da talauci da ya yi katutu tsakanin jama'a.

https://p.dw.com/p/1HDfc
Hoto: Getty Images/AFP/G. Cacace

Gabannin fara taron makonni biyu kan sauyin yanayi a birnin Paris na kasar Faransa, Paparoma Francanis ya yi wannan furuci ne a wani jawabi cikin harshen spaniyanci da ya gabatar a dakin taro na offishin MDD da ke birnin Nairobi. Wannan na a bangaren ci gaban ziyarar da shugaban Katolikan ke yi a wasu kasashe uku na Afirka. Ya zabi nahiyar da ta fi kowacce talauci a duniya,domin gabatar da da wannan kira na bukatar cimma matsaya a taron yini biyu kan sauyin yanayi da za'a fara ranar Litinin a birnin Paris, wadda aka yi wa lakabi da suna COP21...

Kenia Nairobi Messe Papst Franziskus Priester
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Zennaro

"Nan da 'yan kwanaki za'a gudanar da muhimmin taro kan sauyin yanayi a birnin Paris, inda al'ummomin duniya za su sake hallara domin fuskantar batutuwan da suka danganci yanayi. Zai kasance abun takaici , kuma mai mummunan hadari, idan aka sanya fifiko akan cimma bukatu na kai, musamman amfani da bayanai wajen kare nasu tsari da ayyuka, a maimakon kyautata rayuwar al'umma".

Paparoma ya lura da cewar duniya na fuskantar yanayin da take da zabi, na ko ta inganta ko kuma ta lalata muhalli, domin acewarsa, ko wane mataki aka dauka walau babba ko karami, daga mutum ko zuwa kungiya, na kulawa da duk wata halitta, hanya ce mai inganci da ke bawa dan Adam damar bayyana bajintarsa. Shugaban Katolikan ya lura da yadda wasu masana kimiyya ke fafutukar kare gandun dajin Congo, wanda fadinsa ya hade kasashe shida, kuma shi ne daji na biyu mafi girma a duniya, wanda ke da muhimmanci nan gaba saboda dumbin albarkatun da ke cikinsa.

Cover CD Ausschnitt Wake up von Papst Franziskus
Hoto: picture-alliance/dpa/Believe Digital

" COP21 na wakiltar muhimmin mataki na inganta sabon tsarin samar da makamashi, ta sabbin dabaru da ake da su ta yadda ba za'a bukaci amfani da sinadran cabon ba, idan ko kuma kadan kawai za'a nema. Muna dauke da alhakin sake tunanin inganta siyasa da tattali, ta yadda za mu yi gyara a irin kura-kuren da ake da su a yanzu cikin lamuranmu".

Shugaban na darikar Katolika kuma ya yi suka da babbar murya dangane da yadda ake amfani da halin talaucin da jam'a ke ciki, wajen biyan na su bukatu. Ya ce ba za'a kawar da kai kan yadda fataucin mutane ke cigaba da bunkasa saboda talauci ba. Kasuwancin bayan fage na albarkatu kamar lu'u lu'u da wasu ma'adinai da suka hada da hauren giwa, da kashe namun daji kamar Giwa, ba bisa ka'ida ba, ka iya ruruta rigingimu na siyasa da miyagun ayyuka da ta'addanci.