1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugune ba ta kare ba a Bangui

April 28, 2014

Kungiyar likitoci na gari na kowa wato Doctors Without Borders a turance da ke aiki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta bayyana cewa an kashe jami'anta uku.

https://p.dw.com/p/1BpK3
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

Kakakin kungiyar Tim Shenk ne ya bayyana hakan inda ya ce an hallaka jami'an ne a garin Nanga Boguila da ke arewa maso yammacin kasar kusa da kan iyakar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar da Cadi. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin gagarumin shiri na tsaro suka samu nasarar fitar da Musulmin kasar sama da 1,300 daga babban birnin kasar Bangui. Tsawon watanni dai Musulmin na fuskantar kisa da barazana daga tsagerun kungiyar Anti Balaka ta Kiristoci da ke dauke da makamai sakamakon yakin basasar da ya barke a kasar tun bayan da kungiyar 'yan tawayen Seleka ta Musulmi ta jagoranci kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Francois Bozize.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal