Tsugune ba ta kare ba a zaben kwango

Zanga-zanga ta barke a Kwango bayan bayyana Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa. Martin Fayulu wani dan takarar adawa ya yi watsi da sakamakon.

Kasar Kwango na fatan kafa tarihi a karon farko na mika mulki bisa tafarkin Dimukaradiyya daga gwamnatin farar hula zuwa wata. Sakamakon zaben dai ya zo da ba zata inda dan takarar adawa Felix Tshisekedi ya yi nasara.

Duk da cewa babu wani gagarumin tashin hankali da aka fuskanta a yawancin yankunan kasar ta tsakiyar Afirka, al’ummar sun zabi zaman lafiya da karbar nasarar Tshisekedi domin kawo karshen mulkin shugaba Joseph Kabila.

A hannu guda dai manazarta na ganin cewa kalubalantar sakamakon da dan takarar adawa Martin Fayulu ya ci alwashin yi a gaban kotu na iya jefa kasar cikin rudani.

Cochin Katolika wanda ke da karfin fada a ji da kuma ya baza jami’ai 40,00 domin sa ido akan zaben yace sakamakon da aka baiyana bai yi daidai da nasa sakamakon da ya tattara ba.