1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugune ba ta kare ba a Zirin Gaza

August 8, 2014

Tattaunawar da aka yi tsakanin Falasdinawa da Isra'ila a kasar Masar ta watse ba tare da cimma wata matsaya ba.

https://p.dw.com/p/1CrC3
Hoto: Reuters

Tattaunawar da Masar din ke shiga tsakani ta gaza haifar da da mai ido ne bayan da kungiyar Hamas ta ce Isra'ila ba ta amince da ko da guda daga cikin bukatunta da ta gabatar ba. A nan gaba kadan ne dai yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki uku da bangarorin biyu suka cimma za ta kare bayan da suka gaza amincewa da kara wa'adin yarjejeniyar.

A hannu guda kuma mahukuntan Isra'ila sun bayyana cewa kungiyar Hamas ta ci gaba da jefa rokoki zuwa Isra'ilan tun da sanyin safiyar Jumma'ar nan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo