1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brexit: Siyasar Birtaniya ta shiga rudani

Abdullahi Tanko Bala
January 16, 2019

Firaministar Birtaniya ta sha kaye mafi muni a tarihin kasar inda 'yan majalisar dokoki suka kada kuri'ar da rinjayen kuri'u 230 na yin fatali da yarjejeniyar da ta cimma da tarayyar Turai kan ficewar kasar daga EU.

https://p.dw.com/p/3BeCB
England Brexit Theresa May
Hoto: picture-alliance/dpa/House Of Commons

'Yan majalisar Birtaniyar sun yi watsi da daftarin yarjejeniyar da gagarumin rinjaye a kuri'ar da suka kada a jiya Talata inda 'yan majalisa 432 suka kada kuri'ar rashin amincewa yayin da yan majalisa 202 suka goyi bayan daftarin.

Da ta ke jawabi bayan zaben Firaminista Theresa May ta yi kira ga majalisar ta cimma matsaya kan batun na Brexit na ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai.

Ta ce " Kowace rana da ta wuce ba tare da warware wannan batu ba, na nufin kara shiga yanayi na rashin tabbas da kunci da kuma rudani. Gwamnati ta ji abin da majalisa ta ce amma kuma ina kira ga yan majalisa daga dukkan bangarori su saurari bukatun jama'ar Birtaniya wadanda ke son ganin an warware wannan batu, su kuma hada hannu da gwamnati domin yin wannan aiki."

Shugaban Jam'iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn ya gabatar wa majalisar dokokin da bukatar kada kuri'ar rashin amanna akan gwamnatin a yau Laraba, lamarin da zai iya jawo gudanar da zabe gabanin wa'adi.

Mahawara  a majalisar Birtaniya
Mahawara a majalisar BirtaniyaHoto: picture-alliance/dpa/J.-F. Badias

Ya ce " Wannan sakamako shi ne kaye mafi muni da wata gwamnati a kasar nan ta fuskanta cikin shekaru 95 da suka gabata. Wannan mummunan kaye ne ga wannan gwamnati bayan gazawar da ta yi a tattaunawar da ta shafe shekaru biyu tana yi akan batun ba tare da cimma wata nasara ba.

Majalisa ta riga ta yanke hukunci akan  shirinta na Brexit kuma hukunci ya tabbata. Abin da ke gaban mu shine cewa gwamnati ta rasa amincin majalisa a kasar nan, a saboda haka ina gabatar da kudirin kada kuri'ar rashin amanna akan wannan gwamnatin".

Idan Theresa May ta tsallake kuri'ar rashin amannar, a cewar ofishinta za ta nemi hadin kan yan majalisar dokoki na jam'iyyarta da manyan jami'ai na jam'iyyun adawa domin tsara wata sabuwar yarjejeniya inda a ranar Litinin za ta gabatar wa majalisar dokoki tsarin yadda ta ke gani za a sami cigaba game da shirin ficewar

Shugaban jam'iyyar LabourJeremy Corbyn
Shugaban jam'iyyar Labour Jeremy CorbynHoto: Reuters/P. Noble

A ranar 29 ga watan Maris aka tsara Birtaniya zata fita daga kungiyar EU. Sai dai a baiyane ta ke cewa lokaci na neman kure wa Birtaniyar a cewar Michel Banier babban mashawarcin kugiyar tarayyar Turai kan Brexit.

 Ya ce " Yanzu ya rage ga Birtaniya ta sanar da mu mataki na gaba kuma mu a bangaren mu za mu kasance a hade da kwakkwarar kudiri don cimma yarjejeniya."

Kungiyar Tarayyar Turai dai da gwamnatocin Turan sun yi kashedin cewa watsi da daftarin da majalisar dokokin Birtaniyar suka yi ya jefa kasar cikin yiwuwar fita daga kungiyar ba tare da kyakkyawar shiri ba.