1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

170413 ZAR Konflikt

April 18, 2013

Tun bayan da 'yan tawayen Seleka su ka kwaci iko a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, dubunan mutane ke barin gidajensu, mussamman a Bangui babban birnin kasar, domin kauracewa tashe-tashen hankula.

https://p.dw.com/p/18Iju
Chief of the SELEKA rebel alliance Michel Djotodia sits on January 17, 2013 in Bangui during a ceremony. Opposition figure Nicolas Tiangaye was officially appointed today Prime Minister of the Central African Republic's new national unity government, President Francois Bozize said after a ceremony in the capital Bangui. The announcement was in line with a peace deal struck between the ruling party, the Seleka rebels and the democratic opposition in the Gabonese capital of Libreville last week.
Michel DjotodiaHoto: Getty Images

Kimanin wata guda kenan da 'yan tawayen Seleka suka hambarar da shugaba François Bozize daga karagar mulkin Jamhuriya Afirka ta Tsakiya, a lokacin da suka karbi mulki sun yi alkawarin samar da kwanciyar hankali cikin kasa, to saidai ya zuwa yanzu al'amuran tsaro sun kara tabarbarewa, sannan jama'a ta shiga cikin wani halin kunci rayuwa.

Tun bayan da 'yan tawayen Seleka suka kwaci iko a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ko wace rana dubunan mutane ke barin gidajensu, mussamman a Bangui babban birnin kasar, domin kauracewa tashe-tashen hankula.Tashin hankali na baya-bayan ya wakana a karshen makon da ya gabata, inda kungiyar Bada Agaji ta Kasa da Kasa wato Red Cross ta ce akalla mutane 17 suka rasa rayuka sannan da dama suka ji raunuka.

A wata unguwa mai suna Boy-Rabe dake birnin Bangui har yanzu mutane na rayuwa jini kan akaifa, kamar yadda wannan matar da ta samu mafaka a wata asibiti ta ke baiyani:

Seleka rebel coalition member, which launched a major offensive last month, hold on January 10, 2013 a position in a village 12 kms from Damara, where troops of the regional African force FOMAC are stationned. Rebels in Central Africa on March 22, 2013 were advancing on the capital Bangui after forcing their way through a key checkpoint manned by international forces, a military source told AFP. The rebels from the Seleka coalition had shot their way through the Damara checkpoint, some 75 kilometres (47 miles) north of the capital, around 1100 GMT, said a source with the Multinational Force of Central Africa (FOMAC) which was manning the roadblock. AFP PHOTO/ SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

" 'Yan bindiga su na bi gida-gida su na kwashe dukiyar jama'a, kuma su na dukar duk wanda yayi gardama, abin babu kyan gani, saboda haka ne muka gudo anan kuma a yanzu ba mu tunanin komawa sai mun tabbatar da kura ta lafa."

Unguwar Boy-Rabe na matsayin sansanin magoya bayan hambarraren shugaban kasa Bozize.Kungiyoyin kare hakkokin bani Adama na kasa da kasa, sun zargi 'yan Seleka da aikata kisan gilla ga mazauna wannan unguwa.A cewar Andreas Mehler, wani masani game da harkokin tsaro a Afirka dake Cibiyar GIGA ta birnin Hamburg wannan ta'asa na faruwa dalili da kasawar sabuwar gwamnati:

"Cemma ai an san a rina! domin Kungiyar 'yan tawayen Seleka, taho na taho ne tsakanin kungiyoyin tawaye barkatai, saboda haka babu wanda ke iya tsawata musu game da barnar da suke aikatawa.Abin da kamar wuya wannan sabuwar gwamnati ta yi nasara magance matsalar hare-haren da 'yan tawayen Seleka ke shiryawa".

Saidai a nata bangare, gwamnatin Michel Djotodiya ta na zargin magoyan bayan hambarraren shugaban kasa da aikata wannan ta'asa a birnin Bangui da kewaye, sannan ta yi kira ga Faransa da kungiyar kasashen yankin Tsakiyar Afirka su taimaka mata domin tabbatar da doka da oda kamar yadda ministan yada labarai Christophe Gazembeti ya shaidar:

Supporters of Central African Republic President Francois Bozize and anti-rebel protesters hold banners as they gather for an appeal for help by Bozize, in Bangui December 27, 2012. Bozize on Thursday appealed for France and the United States to help push back rebels threatening his government and the capital, but Paris said its troops were only ready to protect French nationals. The exchanges came as regional African leaders tried to broker a ceasefire deal and as rebels said they had temporarily halted their advance on Bangui, the capital, to allow talks to take place. White banner on bottom right reads, "France, help us recover peace. You colonised us." Picture taken December 27, 2012. REUTERS/Stringer (CENTRAL AFRICAN REPUBLIC - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

"A tsawan watani da dama shugaba Bozize ya rarrabawa matasa makamai.Wannan makamai sukje amfani da su yanzu cikin aiyukan fashi da kwasar ganimar jama'a"

Wannan saban yanayi da Jamhuriya Afirka ta Tsakiya ta sami kanta ciki, ya haifar da matsaloli masu tarin yawa, wanda suka cilastawa akalla mutane dubu 40 shiga gudun hijira a kasashe makwafta kamar su Chadi,Kamaru da kuma Kongo Tom Roth, jami'i ne a Kungiyar Likitocin Bada Agaji na Kasa da Kasa wato "Medecins sans Frontieres" ya shaida halin da mutanen ke ciki:

"Al'amarin ya na tayar da hankali, sace-sace da kai hare-hare sun zama ruwan dare.Mutane suna tsoran zuwa likita kokuma wurin aiki.

Central African Republic President Francois Bozize (centre L, in blue) speaks to a crowd of supporters and anti-rebel protesters during an appeal for help, in Bangui December 27, 2012. Bozize on Thursday appealed for France and the United States to help push back rebels threatening his government and the capital, but Paris said its troops were only ready to protect French nationals. The exchanges came as regional African leaders tried to broker a ceasefire deal and as rebels said they had temporarily halted their advance on Bangui, the capital, to allow talks to take place. Picture taken December 27, 2012. REUTERS/Stringer (CENTRAL AFRICAN REPUBLIC - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Babbar matasalr da kasar ke fuskanta yanzu itace rashin gwamnati mai karfi wadda ta ka shimfida tsaro"

Saban shugaban kasa Michel Djotodiya yayi alkwarin shirya zabe a tsukin watani 18, to saidai kamin nan babban kalubale shine tabbatar da tsaro cikin kasa.A wannan Alhamis, Kungiyar Kasashen Yankin Tsakiyar Afrika, ta kiri taron koli a birnin Djamena na kasar Chadi, domin daukar mataki game da halin da Jamhuriya Afirka ta Tsakiya ke ciki.

Mawallafa:Hahn Julia/ Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani