1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tuhumar da akewa tsohon mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu

December 6, 2005
https://p.dw.com/p/BvHj
Tony Blair
Tony BlairHoto: AP

A yau talata ne tsohon shugaban kasar Africa ta kudu, wato Jacob Zuma ya bayyana gaban wata kotu a kasar don amsa tuhumar da ake masa na yiwa wata mace fyade.

Tun dai ba a je ko ina ba Jacob Zuma ya karyata wannan zargi da ake masa da cewa bashi da tushe balle kuma makama.

Wannan dai tuhuma da ake masa tazo ne a dai dai lokacin da ake shirye shiryen gabatar da dashi a gaban kuliya don amsa laifin cin hanci da rashawa, wanda hakan ne ya haifar da cire shi daga mukamin sa na mataimakin shugaban kasa a watan yuni daya gabata.

Rahotanni dai sun nunar da cewa wannan sabon zargi da ake masa da alama ka iya kawo masa cikas na hasashen da yake na zamowa shugaban kasar ta Africa ta Kudu a zabe mai zuwa.

Duk da dai wadan nan zarge zarge da akewa tsohon shugaban , har yanzu shine mataimakin shugaban jamiyyar ANC mai mulkin kasar a halin yanzu, koda yake a yanzu haka yana ci gaba da fuskantar matsin lamba na yin murabus.