1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tuhumar sojin Amurka a Iraqi

August 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuDe

Maaikatar sojin Amurka ta fara tuhumar wani jamiin soji da ake zargi da laifin gallazwa firsinoni, a gidan yarin Abu Ghraib dake Bagdaza babban birnin Iraki .A shekara ta 2004 ne aka bayyana wannan taasa.Sojan da ake tuhuma mai suna Lieutnant Colonel Steven Jordan an gurfanar da shi ne a gaban wata kotu dake jihar Maryland akan laifuffuka hudu da suka hada da cin zarafin firsinoni.Shine aka dankawa alhakin kula da gidan yarin na Avbu Ghraib amma ya musanta cewar yana da hannu a cikin wannan taasa.Yace so ake a shafa masa kashin kaji.An dai yi watsi da wasu laifuffuka da aka zarge da shi da aikatawa bayan janar dake bincike, ya yarda cewa bai nunawa Jordan hakkinsu na yi kawaici akan zargin da ake yi masa ba.