1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da ranar 'yanci a Najeriya

Ubale MusaOctober 1, 2014

Shugabannin al'ummar Tarayyar Najeriya sun kai ga bikin cikar kasar shekaru 54 da samun kai cikin hali na rudani da ma kaskantar da kawuna.

https://p.dw.com/p/1DONQ
Nigeria - 54. Unabhängigkeitstag
Hoto: DW/U. Musa

Ko bayan faretin da akasin abun da ke akwai can baya ya kare ne a cikin fadar gwamnatin kasar ta Aso rock tare da yankan alkakin cikar kasar shekaru 54 cikin farin ciki da annashuwa a fadar shugaban kasar da tun da safiyar Larabannan ya kai ga wani jawabi na musamman ga 'yan kasa.

Jawabin kuma da a cikin sa Jonathan din ya ce kasar ta yi nisa ga batu na tattalin arziki dama zamantakewar ta duk da jerin matsaloli irin na su Boko Haram din da ke cin tuwo cikin kwaryarta a yanzu.

Tuni dai ra'ayi ke banbanta a tsakanin manya da kanana na 'yan kasar da ke kallon kasar da ido daban-daban, Aliko |Dangote dai na zaman mafi arziki cikin kasar da ke kallon dama ga kasar duk da halin rashin tsaron da ke a cikinta.

Nigeria - 54. Unabhängigkeitstag
Hoto: DW/U. Musa

“Idan ka duba abun da ya faru a Japan kana ganin dutse ne ya taso ya rufe mutane suka mutu,da dama waddanan masifu Allah ya dauke mana. Kuma ba zai yiwu ace ba ka da wata jarraba, dole ne a samu hanyar Jaraba, amma duk da wannan matsaloli irin na su Boko Haram Allah zai ba mu hanyar maganinsu”

To sai dai in tuni ta yi zaki a tunani na Dangote, ga irinsu tsohon shugaban majalisar wakilan kasar Ghali Umar na Abba, kauda kabilanci a shugabanci na zaman mafita ga burin kasar na samun sauyi.

"A ko yaushe a kowane lokaci, ya kamata shugabanci ya amince cewar duk abun da za'ayi, ayi shi bisa adalci. Shugaba ya yi la'akari a kowane lokaci cewar adalci shi ne kawai zai ja masa soyyaya.”

Nigeria - 54. Unabhängigkeitstag
Hoto: DW/U. Musa

Soyyayya a cikin adalci ko kuma kokari na nunin fifiko dai na shekaru 54, sun kasance a cikin rabuwar da babu irin ta a tsakanin kudu da arewacin kasar da ma manyan addinanta biyu.

Ko bayan nan kuma a fadar Senata Kabiru Gaya da ke zaman jigo a adawar kasar babu tsuntsu kuma tarkon ma ya kama hanya ta bata ne ke zaman karatun 'yan mulkin kasar a halin yanzu.

“ Muna fitar da manja da su gyada da sauran abubuwa, amma yanzu ina waddanan abubuwa: yadi shigo da shi muke. Alamar zaman lafiyar da ke tutar Najeriyar ma yanzu ba ya aiki, ba zaman lafiyar ba noman saboda rashin kulawa na shugabannin da suka taho”