1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da Thomas Sankara

Hauwa Abubakar AjejeOctober 15, 2007

A yau ake tunawa da zagayowar shekaru 20 da kashe tsohon shugaban kasar Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/BtuN

A ranar 15 ga watan oktoba na 1987 aka kashe Thomas Sankara uban juyin juya hali na Burkina Faso cikin wani juyin mulki daya kawo tsohon abokinsa Blaise Campaore bisa karagar mulki.

Ana saka sunan Sankara cikin jerin masu kishin Afrika kamar su Kwame Nkurumah ba Ghana da Julius Nyerere na Tanzani da kuma Jomo Kenyata na Kenya.

Amma shekaru 20 bayan mutuwarsa magajin nasa bai da damu a hukumance ya tuna da tsohon abokin nasa ba,wanda a kokarinsa na kara manatawa da mulkin mallaka ya canzawa kasar daga Upper volta zuwa Burkina faso a 1984.

A maimakon haka gwamnatin Campaore ta zabi tayi bikin tunawa da zagayowar shekaru 20 da kafuwarta inda aka gudanar da fareti da babban taro kan ci gaban demokradiya a Afrika,tare da gaiyatar shugabanin Afrika da dama.

An kuma shirya wani gagarumin biki na mawaka a ranar 20 ga wannan wata.A daya hannun kuma abikan Thomas sankara suma sun shirya nasu babban taro a birnin Ouagdougou sai dai kuma a cewarsu jamian gwamnati sun kawo cikas wajen samun dakin da zasu gudanar da wannan taro.

Hakazalika zaayi bikin wake wake na mawaka da dama da suka hada da Malcolm wanda ya baiyana Sankara da cewa shahidi ne kuma mai fada a ji ne.

“idan yana magana kowa sauraronsa yake ko mata masu sayarda tumatir a ksuwa Sankara mutum ne mai ilmi a kowane bangare,ba zaa taba mantawa da sankara ba”

Haka shima wani mai bada labarum gargajiya da ake kira KPG yace Sankara mutun ne mai son aladu kuma mai martaba kwarai.

“Thomas sankara a raayi ne ba dan siyasa bane aa mutum ne dan gargajiya,wanda ya taimakawa kasarsa ta fanning aladu.Cikin shekaru Sankara ya nuna gaskiya da adalci wanda wasu basu cimma ba cikib shekaru 25,babu cin hanci a wurinsa”KPG

Ba mawaka kadai suke martaba Thomas Sankara ba har ma dam asana, ainda Luc Marius Ibiriga wani farfesa a fannin sharia yace Sankara mutum ne mai mutunci da kawrjini a zamaninsa.

Har ya zuwa yanzu shekaru 20 bayan mutuwar tasa,babu wani takamaimen bayani kan yadda mutumin da har yanzu ake girmamawa ya rasa ransa.haka kuma ana ci gaba da gudun tattaunawa akai.