1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunisiya ta hana jiragen Libiya shiga kasarta

Pinado Abdu WabaMarch 24, 2015

Sakamakon fargabar da take yi kan yaduwar rikicin Libiya zuwa kasarta, Tunisiya ta dakatarda jiragen Libiya daga shiga kasar nata.

https://p.dw.com/p/1EwIx
Tunesien Tunis Präsident Beji Caid Essebsi Statement Terroranschlag
Shugaba Beji Caid EssebsiHoto: Reuters/Z. Souissi

Tunisiya ta sake rufe hanyoyin sufurinta na sama da Libiya, kwanaki kadan bayan da ta amince jiragen Libiyan da suka shafe watanni shidda a kasar su koma Tripoli. Wannan matakin ya zo ne sakamakon harin da aka kai gidan tarihin Tunis, wanda ya kai ga hallakar 'yan yawon bude ido 20. Majiyoyin tsaro sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa biyu daga cikin 'yan bindigan sun sami horo ne a wani sansanin horaswar IS da ke Libiya.

Tunisiya na fargabar kada tashe-tashen hankulan da suka addabi Libiya su shafeta musamman ganin yadda har yanzu, bangarori biyu ke kokuwar rike madafun ikon kasar ko bayan shekaru hudu da mutuwar Mu'ammar Gaddafi.

Wannan mataki zai kuntatawa 'yan Libiya da dama wadanda sukan tsere zuwa Tunisiya domin kauracewa matsalar tsaron kasarsu