Tunisiya ta katse hanzarin 'yan ta'adda
October 20, 2014Talla
Mahukuntan kasar Tunisiya sun bayyana dakile hare-haren tsageru kan jami'an diplomasiya da harkokin tattalin arzikin kasar, a makonnin da suka gabata.
A wannan Litinin ministan harkokin cikin gida Lotfi Ben Jeddou ya ce 'yan ta'addan sun yi yunkurin kai hare-haren bama-bamai da motoci, kan jakadun kasashen ketere, da wasu kamfanoni amma jami'an tsaro suka dakile, sai dai jami'in bai yi karin haske ba. Tuni ma'aikatar cikin gidan ta ce za a jibge jami'an tsaro kimanin 46,000, domin tabbatar da doka da oda, yayin zaben mako mai zuwa a kasar ta Tunisiya da ke yankin arewacin Afirka.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba