1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunusiya ta gina shinge kan iyaka da libiya

Gazali Abdou TasawaFebruary 7, 2016

Shingen mai tsawon kilomita 200 na da burin kare kasar daga hare-haren ta'addanci irin wadanda ta fiskanta a shekara ta 2015, hare-haren da Tunusiyar ta ce masu aiwatar da su na fitowa ne daga kasar ta Libiya.

https://p.dw.com/p/1HrEP
Tunesien Libyen Anti-Dschihadisten-Zaun
Hoto: Getty Images/AFP/F. Belaid

Gwamnatin kasar Tunusiya ta sanar a wannan Asabar da kammala aikin ginan shingen tsaro tsakanin kasar tata da ta Libiya.

Da yake tsokaci a gaban manema labarai lokacin da ya ziyarci kan iyakar a wannan Lahadi, Ministan tsaron kasar ta Tunusiya Farhat Horchani ya ce shingen wanda ke da tsawon kilomita 200 na da burin kare kasar daga jerin hare-haren ta'addanci irin wadanda ta fiskanta a shekara ta 2015, hare-haren da ya ce masu aiwatar da su na fitowa ne daga kasar ta Libiya.

Ministan tsaron kasar Tunusiyar ya ci gaba da cewa shingen wanda aka gina da tudunnan kasa da magudanan ruwa za a kuma karfafa shi da na'urorin tsaro wadanda kasashen Jamus da Amirka za su taimaka wa kasar ta tunusiya da su.