1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunusiya ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel

Gazali Abdou TasawaOctober 9, 2015

Rukunin wasu kungiyoyi hudu na kasar Tunusiya wadanda suka taka rawa wajen sasanta bangarorin kasar bayan juyin juya hali sun samu kyautar Zaman lafiya ta Nobel.

https://p.dw.com/p/1Glhk
Tunesien Friedensnobelpreisträger das tunesische Quartett für den nationalen Dialog
Hoto: picture-alliance/dpa/C. B. Ibrahim

Rukunin wasu kungiyoyin da suka taka rawa wajen sasanta rikicin kasar Tunusiya ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ta wannan shekara ta 2015 wacce kwamitin bada kyautar Nobel da ke birnin Oslo ya bada a wannan Jumma'a.

Rukunin wanda ya hada da babbar kungiyar kwadago ta kasar ta UGTTda ta manyan 'yan kasuwar kasar wato Utica da babbar kungiyar kare hakkin dan Adam ta LTDH da kuma kungiyar Lauyoyin kasar ya samu wannan kyauta ce a sakamakon gudummawar da ya kawo, wajen sasanta masu kishin Islama da sauran 'yan adawar kasar ta Tunusiya ta hanyar lumana dama dora kasar kan turbar demokaradiyya bayan juyin juya halin da aka gudanar a kasar a shekara ta 2011.

Tuni dai kasashe daban daban musamman na Turai suka bayyana gamsuwarsu kan zabin bayar da wannan kyauta ta Nobel ga 'yan kasar Tunusiyar wanda suka ce suna fatan za su zamo wani abin misali wajen warware rigingimun da ke tasowa a kasashe da aka samu juyin juya hali.