1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai: China na karan tsaye kan matsalolin yana yi

Zainab Mohammed AbubakarDecember 10, 2015

Miguel Arias Canete ya zargi China da kin amincewa shawarwarin da aka gabatar don cimma rage hayaki mai guba da masa'antu suke fitarwa cikin shekaru biyar.

https://p.dw.com/p/1HLac
EU Canete PK zur Energiepolitik
Hoto: picture-alliance/epa/J. Warnand

Babban direkta a sashin kula da muhalli na MDD ya bayyana fatan cimma tudun dafawa a daidai lokacin da ake kwanakin karshe na karkare taron lalubo hanyoyin da za'a kalubalanci matsalar dumamar yanayi a a birnin Paris. Achim Steiner ya nunar da cewar, ko da daga karshe an gano bakin zaren matsalar da ta addabi duniya zai dauki lokaci kafin a cimma warware shi, ai dai kwalliya ta biya kudin sabulu.

"Ana iya cewar mun kai wani matakin na batutuwa da suka fi daukar hankali kuma masu hadari. Batutuwan da suka tara mu anan, wadanda kuma dole ne mu cimma warwaresu. Abun da suka rage mana basu fi uku zuwa hudu ba, wadanda ke bukatar tsarin siyasa wajen warwaresu. Da fatan dukkan wadanda abun ya shafa zasu bada hadin kai, domin gano bakin zaren".

A tunanin Steiner dai matsalar ta danganci banbanta kasashe masu cigaba da matalauta. Tuni dai babban jami'in Turai a wajen taron na Paris ta zargi kasar China da yin karan tsaye ga shawawarin da aka gabatar wa kasashe na aiwatar da yarjejeniyar rage hayaki mai guba da suke fitarwa a kowace shekara biyar.

Kwamissionan da ke kula da yanayi na Turai Miguel Arias Canete, ya fadawa taron manema labaru a Paris cewar, aiwatar da wannan yarjejeniya shi ne hanya daya tilo da zai ceto duniya daga barazanar sauyin yanayi. Sama da kasashe 180 nedai suka gabatar da manufarsu na rage hayaki mai guba da masana'antunsu ke fitar nan da shekara ta 2020.