1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadakar Turai da Afirka a bunkasar arziki

Abdullahi Tanko Bala YB
December 18, 2018

Shugabanni da manyan jami'an gwamnati daga kasashe fiye da 50 na Kungiyar Tarayyar Turai da Afirka sun gudanar da taron koli a Talata a birnin Vienna domin karfafa kawancen tattalin arziki da zuba jari.

https://p.dw.com/p/3AKVb
Österreich EU-Afrika-Forum in Wien
Jean-Claude Juncker na Hukumar EU da Paul Kagame da Sebastian Kurz Hoto: Getty Images/AFP/J. Klamar

Taron wanda ya gudana karkashin jagorancin shugaban gwamnati na kasar Ostiriya Sebastian Kurz wanda kasarsa ke rike da shugabancin karba karba na Kungiyar Tarayyar Turai da kuma shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame da ke jagorantar Kungiyar Tarayyar Afirka AU ya mayar da hankali ne kan fasahar na'urorin sadarwa na zamani wato digital. Taron ya zo ne watanni shida bayan wani taron koli na shugabannin Turai da ya amince cewa magance gudun hijira daga Afirka na bukatar daukar matakai da za su kawo sauyi a yanayin walwala da jin dadin rayuwar jama'a da bunkasar tattalin arziki a kasashen Afirka.

A bisa alkaluman kididdigar na Kungiyar Tarayyar Turai, Afirka ita ce nahiya ta uku mafi karfi wajen huldar kasuwanci da kasashen Turai inda ta ke bin bayan China da Japan. Kungiyar Tarayyar Turan dai na fatan habaka kawancen tattalin arziki da kasashen Afirka domin cimma yunkurin da kasar China ke yi a nahiyar a cewar shugaban gwamnatin Ostiriya da kasarsa ke rike da shugabancin karba karba na Kungiyar EU.

Wien EU-Afrika-Gipfel
Shugaban Ruwanda Paul Kagame da Sebastian Kurz na OstiriyaHoto: picture-alliance/APA/H. Punz

Shi ma dai shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya ce duk da cewa China ta yi nisa a huldarta da Afirka, amma kasashen Turai ba su makara ba. Akwai alaka mai karfi ta tarihi tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar Tarayyar Afirka duk da cewa wasu sun kasance ne na zamanin jahiliyya, amma wannan ba zai hana karfafa hulda a tsakanin nahiyoyin ba a cewar ministan sadarwa na kasar Namibiya Stanley Simataa. Shi ma ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso Alpha Barry jaddada fata ya yi cewa kawancen da ake so a kulla zai amfani nahiyoyin biyu. 

A karshe ana fata wannan taro zai samar da dangantaka mai karfi tsakanin kasashen Turai da Afirka ta musayar fasaha da cinikayya da samar da ayyukan yi da gina al'umma mai nagarta da kuma aiwatar da shirin raya kasa mai dorewa. Kamfanoni fiye da 1000 na Turai da kuma sabbin kamfanoni masu tasowa na Afirka suka halarci taron.