1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai da Afirka za su yi aiki tare

Sabine FaberApril 3, 2014

Wannan ita ce sanarwa ta ƙarshe da shugabannin ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai da na Afirka suka bayyana a birnin Brussels na Beljium a ƙarshen taronsu

https://p.dw.com/p/1BbeC
EU Afrika Gipfel Merkel 02.04.2014 Brüssel
Hoto: Reuters

Shugabannin ƙasashen Nahiyar Turai da na Afirka sun kammala wani taron ƙolli na kwanaki biyu a birnin Brussels na ƙasar Beljium tare da cimma nasarar samun daidaituwar baki a kan wasu muhimman batutuwan na hulɗa ta kasuwanci da sauransu. Sai dai kuma a wani ɓangaren an samu saɓani tsakanin ƙasashen a kan batu 'yan luwaɗi da 'yan maɗigo.

Kwaliya ta biya kuɗin sabulu ga dukkanin sassan biyu

Za a iya cewar kwaliya ta biya kuɗin sabulu, ko da shi ke ma har yanzu da sauran batutuwan da ƙasashen ba su kammala tattaunawa ba. Amma duk da haka su dukkaninsu sassan biyu sun yi amanar cewar suna buƙatar juna domin samun ci ga ba. An dai kwashe kwanaki biyu shugabannin na tafka mahawara a kan batutuwan da suka shafi hulɗa da batun baƙi yan ci rani da rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma rashin tsaro da ake fama da shi a wasu yankunan nahiyar. Abin da shugaban hukumar Ƙungiyar Trayyar Turan José Manuel Barosso ya ce dole ne nahiyoyin biyu su yi cuɗe-ni-in-cuɗe-ka domin shawo kan matsalar ta ta'addanci a cikin ƙasashen yankin Sahel.

EUTM Uganda Archiv 2012
Hoto: Bundeswehr

'' Matsala ce da ta shafemu mu dukka idan ta'addanci ya bazu a yankin Sahel ko a yankin Ƙahon Afirka, ko kuma idan aka gasa lura da zirga-zirga baƙi masu ƙaura ' yan ci rani wannan barazana ce ga Afirka da ma Turai.''

Taron ya tattauna batun canji yanayi da na tsaro

Duk da ma irin batun da ya fi ɗaukar hankali a taron shi ne na yaƙin da ake fama da shi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadda tuni shugabanin ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turan suka yi alƙawarin aikewa da sojoji a ƙasar. Babban Sakataren MDD Ban Ki Moon ya yi gargaɗin cewar baya ga waɗannan matsaloli da ake fama da su wani batun da ke ciwo ƙasashen tuwo a ƙwarya shi ne na canci yanayi. Batun da shugaban ƙasar Chadi Idriss Deby ya ce Afirka ita ce ke biya da tsada.

EU Afrika Gipfel in Brüssel Mohamed Ould Abdel Aziz und Herman Van Rompuy
Hoto: Reuters

''Sauyin yanayi abu ne da ya shafi duniya baki ɗaya amma nahiyar da ta fi shan wahala a kan wannan al'amari, ita ce nahiyar Afirka wanda tabkuna da gokuna a nahiyar na ƙafewa ko ma ɓacewa.''

An yi hannun riga tsakanin shugabannin a kan batun kare hakin tsiraru

Wani batun da ya kasance an yi hannu riga a kansa a wurin saduwar shi ne na tauye hakkin tsiraru wanda galibi ake fuskanta a nahiyar Afirka, na nuna wariya da banbanci ga wasu jama'ar tsiraru masu aikin luwaɗi da maɗigo. A sa'ilin wata lifiyar cin abinci da aka shirya shugabannin a ƙarshen taron an gayato wani mai fafutukar kare hakkin tsirarun, Elio Di Rupo, a gaban shugabannin ƙasashen Yuganda da Najeriya, waɗanda su dukkaninsu ƙasashen a kwanan baya, suka amince da dokoki tsatsaura a kan 'yan luwaɗin da maɗigo. Herman Van Rompuy babban kwamishina na Ƙungiyar ta Tarayyar Turai ya yi tsokaci tare da ƙara jan hankalin shugabannin.

Goodluck Jonathan und Angela Merkel
Hoto: Reuters

''A kwai buƙatar mu yi magana domin muntuta hakokkin bil adama na kowa a Turai da Afirka har ma da na tsiraru.|''

Shugaban ƙasar Faransa dai Francois Hollande ya sanar da wani tsari tare da Jamus a kan wani ƙawancen tsakanin Turai da Nahiyar Afirka, a kan manufofi guda uku: Waɗanda su ne al'amuran tsaro da muhali da kuma ci gaba; wanda shugabar gwamnatin Jamus Angela Mrkel ta ce wani sabon yunƙuri ne na ƙasar a cikin harkokin tsaro a nahiyar Afirka. Inda tuni suke da sojoji a Mali da Jamhuriyar Afirka taTsakiya. Abin jira a gani dai shi ne irin tasirin da zai biyo bayan taron.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Hasselbach Christoph/Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar