1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai: Merkel da Macron na son tabbatar da hadin kai

Suleiman Babayo
May 16, 2017

Sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce zai yi aiki da takwararsa ta Jamus Angela Merkel wajen ganin an samu karin hadin kai a kasashen da ke cikin kungiyar nan ta EU.

https://p.dw.com/p/2d3SH
Emannuel Macron Angela Merkel Berlin
Hoto: Reuters/F.Bensch

Duk da cewar shugabannin biyu na 'yan banbance-banbance amma dai a wani fannin sun fuskanci alkibla guda wadda ke da nasaba da ganin an samu karin hadin kai a nahiyar Turai. Wannan dai ta kara fitowa fiki ne bayan da Shugaba Macron ya ziyarci Merkel a Berlin jim kadan bayan da ya ya sha rantuwar kama aiki. Shugabar gwamnatin Jamus dai ta jima ta na fafutuka wajen ganin Turai ta cigaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya musamman ma dai bayan da Burtaniya ta kada kuri'a ta ficewa daga cikin kungiyar.

Emmanuel Macron und Angela Merkel Berlin
Hoto: Reuters/F.Bensch

Shi ma dai Macron na da wannan akida ta ganin Kungiyar EU ta cigaba da kasancewa yadda taka. Ba ma dai Macron ba, sauran shugabannin da suka gabace shi musamman ma dai Francois Hollande sun sha nanata aniyarsu ta son ganin hadin aki ya yaukaka a nahiyar Turai musamman ma dai lokacin da aka rika samun sabani tsakanin wasu kasashe da cikin wannan kungiya.

To baya ga batu na hadin kan Turai, Macron da Merkel sun lashi takobin ganin lamura a daidaita a Faransa, inda Merkel ta sha alwashi dafa masa wajen ganin ya cimma nasara. Wannan ne ma ya sanya Claire Demesday da ke sharhi kan lamuran da ke faruwa a Faransa cewar "tattaunawar samar da sauye-sauye a Faransa da Macron ke yi da Jamus aba ce da ake tsammani za ta yi kyau."

Yanzu haka dai masana da ma al'ummar kasashen Jamus da Faransa da na nahiyar Turai na zuba idanu don ganin yadda wannan hadin kai tsakanin Merkel da Macron zai yi tasiri game da hadin kan Turai wadda ke fuskantar kalubale da dama ciki kuwa har da na tsaro da kuma na tattalin arziki.