1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ture-ture a Abuja ya haddasa rasuwar mutane bakwai

March 15, 2014

Mutane da dama ne suka taru a babban filin kwallon kafa na Abuja a wata jarrabawar daukar jami'an tsaro na kan iyaka da shige da fice inda aka samu ture-ture.

https://p.dw.com/p/1BQJG
Hoto: picture-alliance/dpa

Cikin wannan filin kwallo ne aka shirya daukar ma'aikata, na jami'an binciken kan iyakoki wato "Immigration" a wannan Asabar din, inda aka samu ture-turen, da ya haddasa mace-mace: Wssu kuma da dama sun jikkata, wadanda aka fice da su ya zuwa babban asibitin birnin na Abuja, a cewar jami'in wannan Asibiti Tayo Haastrup. Sai dai kuma bai ba da adadi ba, amma wakilin kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP dake asibitin ya kidaya akalla gawarwaki bakwai.

Ko da yake ba a san adadin mutanen da ke cikin wannan filin kwallo ba yayin ture-turen, amma wani daga cikin wadanda suka samu tsira da rayukansu, ya ce kofa daya ce aka bude ta wannan filin kwallo mai daukan akalla mutun dubu 60.

A cewar jami'in kiwon lafiya na wannan babban asibitin na Abuja, Tayo Haastrup wadanda suka dan daidaita daga cikin masu jin ciwon, sun tura su ne ga sauran asibitoci domin su samu kula da sauran mutanen da ake ci gaba da kawowa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mahammad Nasiru Awal