1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya na ƙarfafa dangantaka da Afirka

January 8, 2013

A wani mataki na ƙara haɓɓaka wannan dangantaka, Firaministan Turkiyya Recep Tayyib Ergogan ya na rangadin wasu ƙasashen Afirka guda uku a wannan mako.

https://p.dw.com/p/17GAW
Hoto: Reuters

Kasashen Afirka da Firaministan na Turkiyya ke kai wa ziyarar sun haɗa da Gabon, Senegal da kuma Jamhuriyar Nijar.

Tun ranar Lahadin da ta gabata, Recep Tayyib Erdogan ya shiga wannan rangadi tare da wata babbar tawaga da ta ƙunshi manyan 'yan kasuwar Turkiyya. Bayan China da Indiya, Turkiyya ke sahu na ukku daga jerin sabbin ƙasashe dake ƙara samun angizo da ƙarfin faɗa aji a nahiyar Afirka. Tun shekarar 1998 Turkiyya ta ɓullo da sabon shirin kutsawa a dama da ita a ƙasashe da dama na nahiyar Afirka, ta fannonin cinikayya diplomasiya da sauran ɓangarori na ma'amalar ƙasa da ƙasa. A wannan taska, hukumomin Ankara sun ainayar da shekara 2005 a matsayin shekarar ma'amala da Afirka.

Kujerar 'yar kallo a zauren taron AU

A wannan lokaci wani Firaministan Turkiyya ya kai rangadin farko a ƙasashen Afrika ta Kudu da Ethiopiya kamin daga bisani ƙungiyar Tarayya Afrika ta baiwa Turkiyya kujera 'yar kallo.

Gero Erdmann masani ne game da nahiyar Afirka, a cibiyar nazarin siyasar ƙasa da ƙasa ta GIGA da ke birnin Hamburg na Tarayya Jamus, ya baiyana tushen sabuwar ma'amala tsakanin Turkiyya game da nahiyar Afrika:

Ali Bongo Ondimba, neuer Präsident von Gabun
Shugaban Ali Bongo Ondimba na Gabon, inda Erdogan ya fara yada zangoHoto: AP

"Sabuwar tafiya tsakanin Turkiyya da Afirka na da nasaba da siyasar da Turkiyya ta ɓullo da ita tun ƙarshen yakin cyacar baka, inda kamar sauran manyan ƙasashen duniya, itama ta shiga ƙoƙarin faɗaɗa abokan hulɗoɗinta."

Daga shekarar 2005 zuwa 2012 ofisoshin jikadancin Turkiyya a Afirka sun ƙaru daga huɗu zuwa 17, sannan a yanzu haka ƙasar na da niyar buɗa sabin ofisoshin jikadanci a wasu ƙasashen nahiyar. Ta fannin ilimi Tukiyya na taka mahimmiyar rawa a Afrika, ta hanyar ba matasa damar zuwa karatu a jami'o'inta, ko makarantun kimiyya, da kuma buɗa makarantu a ƙasashen Afrika. Bugu da ƙari ta na bada horo ga limaman addinin Islama.

A halin yanzu dai Afrika ta kasance matsayin babbar abikiyar Turkiyya saboda haka ofsihin ministan harkokin waje ya ƙirƙiro da wata taswira mai bada kulla da mussamman ga Afrika, inji Gülistan Gürbey mai sharhi a wata jami'ar mai zaman kanta da ke birnin Berlin:

"Sabuwar hulɗa tsakanin Turkiyya da Afirka babbar husa'a ce. Ta samo asali daga tarihin zamanin Daular Sarki Othumaniya, wanda yayi amfani da dangantakar al'adu da addini, domin ƙulla ma'amala mai ƙarfi da nahiyar Afirka."

Huldar kasuwanci ta ninka tsakanin Afirka da Turkiya

Daga shekara 2002 zuwa 2011 ma'amalar saye da sayarwa tsakanin Turkiya da Afrika ta ninka har sau biyar dalili da zuba jari da gine-gine da kamfanonin ƙasar ke yi a sassa da dama na Afirka, sai kuma uwa uba ɓangaren sutura da kayan masarufi wanda ke shigowa Afrika daga Tukiyya, suka yi tashin gwabran zabi.

Babban burin wannan ziyara da Firaministan Recep tayib Erdowan ya kai Afrika shine ƙara bunƙasa ma'amala tsakanin ɓangarorin biyu, inji Gero Erdmann:

Niger Mahamadou Issoufou
Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar, daya daga cikin kasashen da Erdogan ke rangadiHoto: picture-alliance/dpa

"Kasar na bukatar samun goyan bayan Afirka ta fannin siyasa da diplomatiya a ƙoƙarinta na samun ƙarin ƙarfin faɗa a ji a cikin al'amuran duniya, sannan buri na biyu shine ta fannin tattalin arziki."

A yunƙurin cimma wannan buri, shekara 2011, Turkiya ta shirya babban taro a birnin Ankara inda ta gayyaci dukan ƙasashen Afrika.

Sai dai game da wannan sabuwar tafiya, masu adawa na gwamnatin Turkiya da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani Adama, su na zargin hukumomin Ankara da nuna halayen ko in kula game da batutuwan da suka shafi 'yancin jama'a da wasu shugabanin Afrika suka shahara a kai.

Mawallafa: Yilma Haile / Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal