1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta bayyana dakatar da tura dakaru zuwa Iraki

Suleiman BabayoDecember 8, 2015

Gwamnatin Turkiya ta dakatar da matkin ci gaba da tura dakaru yankin arewacin Iraki amma babu jadawalin janye dakarun da suke kasar yanzu haka.

https://p.dw.com/p/1HJH6
Türkische Armee-Transporter nah der Grenze zu Syrien
Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin kasar Turkiya ta dakatar da tura sojoji cikin yankin arewacin kasar Iraki, amma ta ce ba ta tsara shirin fara janye dakaru ba. Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar da haka bayan mahukuntan Iraki sun nemi yanje dakarun Turkiya da aka tura kusa da yankunan da ke hannun tsagerun kungiyar IS masu neman kafa daular Islama.

Ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu ya tabbatar da wannan mataki lokacin tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Iraki Ibrahim al-Jaafari. Tuni Firaminista Ahmet Davutoglu na Turkiya ya ayyana niyar kai ziyara zuwa Iraki nan gaba kadan, domin kawo karshen sabanin da aka samu tsakanin kasashen biyu.