1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta cafke jagoran Kungiyar Amnesty

June 7, 2017

Taner Kiliç jagoran na Kungiyar Amnesty International a Turkiya ya yi fice wajen caccakar mahukuntan na Ankara kan rashin mutunta 'yanci na fadin albarkacin baki.

https://p.dw.com/p/2eDyL
Italien Protest von Journalisten in Rom
Hoto: picture-alliance/Pacific Press/A. Ronchini

Jagoran Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International a Turkiya, ya zo hannun mahukunta bisa zargin alaka da fitaccen malamin nan Fethullah Gulen, da mahukuntan Ankara ke zargi da zama kanwa uwar gami a kitsa juyin mulki da ya gaza nasara a kasar a shekarar bara.'Yan sanda dai sun cafke lauyan Taner Kiliç tare da wasu 22 a Yammacin birnin  Izmir duk dai bisa zargin alaka da malamin da ke zaune a Amirka kamar yadda Kungiyar  Amnesty ta wallafa a shafinta na intanet.

A cewar sakatare janar na kungiyar ta Amnesty Salil Shetty, ya kamata mahukuntan na Turkiya su gaggauta sakin Kiliç da wasu lauyoyin 22 da aka kama a kuma yi watsi da duk wasu zarge-zarge marasa tushe da ake musu.

Taner Kiliç ya yi fice wajen caccakar mahkuntan na Ankara kan rashin mutunta 'yanci na fadin albarkacin baki a cewar Shetty. Sama da mutane 100,000 ne dai aka kora daga aiki ko aka dakatar da su bisa zargin hannu a juyin mulkin da ya gaza nasara a Turkiya a bara.