1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta ce za ta mayar da martani kan 'yan Jihadin Iraki

June 11, 2014

Turkiya ta ce sojojin sa kai sun yi garkuwa da 'yan kasarta 80 a Mosul dake arewacin Iraki kuma za ta mayar da martani matukan an taba lafiyarsu.

https://p.dw.com/p/1CGxN
Recep Tayyip Erdogan
Hoto: Reuters

Ma'aikatar harkokin wajen Turkiya ta ce sojojin sa kai na wata kungiya da ke da alaka da Al-Kaida suna tsare da 'yan kasar Turkiya 80 da suka sace a wurare biyu da ke birnin Mosul na arewacin kasar Iraki. Ma'aikatar ta ce an yi garkuwa da 'yan kasarta su 49 a karamin ofishin jakadancinta sannan an kai su wani wuri da ke cikin birnin, yayin da 'yan kasar 31 direbobin manyan motoci da aka sace a ranar Talata yanzu haka ana tsare da su a wata tashar samar da makamashi da ke a birnin na Mosul. An jiyo ministan harkokin wajen Turkiya Ahmet Davutoglu na cewa kasarsa za ta mayar da martani mai karfi idan aka taba lafiyar mutanenta. A kuma haklin da ake ciki babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi Allah wadai da garkuwar da 'yan bindiga suka yi da jami'an diplomasiyar Turkiyar a Mosul. A hannu daya kuma ya yi tir da kwace birnin Mosul din da 'yan Jihadin da ke fafatukar kafa kasar Islama a Iraki suka yi a ranar Talata.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo