1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta kaddamar da hare-hare kan IS da PKK

Suleiman BabayoJuly 27, 2015

Gwamnatin Turkiya ta kira taron kungiyar tsaro ta NATO bayan kaddamar da farmaki kan 'yan tawayen Kurdawa da kuma kungiyar IS a Siriya

https://p.dw.com/p/1G535
Türkei Anschlag auf Soldaten in Diyarbakir
Hoto: Getty Images/AFP/I. Akengin

Kasar Turkiya ta kaddamar da farmaki da jiragen saman yaki kan 'yan tawayen Kurdanawa na kungiyar PKK. Haka ya zama gagarumin farmaki tun shekara ta 2011. Akwai tsoron matakin zai iya jefa shirin zaman lafiya tsakanin kasar ta Turkiya da kungiyar PKK cikin hadari. Matakin gwamnatin ya biyo bayan hallaka wasu sojoji biyu cikin yankin Kurdawa.

Tuni Turkiya ta kira taron kungiyar tsaro ta NATO-OTAN bayan hare-haren da ta kaddamar da PKK da kuma kungiyar IS a Siriya, amma kasar ta kawar da yuwuwar tura dakarun kasa domin yaki da IS a Siriya.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nemi Firaminista Ahmet Davutoglu ya ci gaba datattaunawa da al'umar Kurdawa.