1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya na son bude iyaka ga 'yan gudun hijira

February 28, 2020

Kasar Turkiyya ta ce ba za ta iya ci gaba da hana 'yan gudun hijira wucewa ta iyakokinta domin isa TUrai ba bayan kisan sojojinta guda 33 a yankin Idlib na kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/3YbIB
Türkei Pazarkule Flüchtlinge an der Grenze zu Griechenland
Hoto: Reuters/H. Aldemir

Mai Magana da Yawun Jam'iyya mai mulkin Turkiyya ta AKP Omer Celik ne ya sanar da haka a ranar Jumma'a. Wannan sabuwar matsaya ta kasar Turkiyya ta zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa 'yan gudun hijira 300 ciki har da mata da kananan yara na kan hanyarsu ta shiga kasar Girka ta bangaren iyakar Turkiyya da ke Arewa maso Yamma.

Sai dai jim kadan da fitar da wannan matsaya ta Turkiyya, Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta MDD ta ce ba ta samu wani labari a hukumance dangane da yunkurin Turkiyya na sauya manufofinta a kan 'yan gudun hijirar Siriya ba, kuma ba ta samu rahoton wasu 'yan gudun hijira da ke kan hanyarsu ta zuwa kasar Girka ko wata kasa a tarayyar Turai ba.