1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan na son dorewar yarjejeniyar Idlib

Yusuf Bala Nayaya
February 14, 2019

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya sake jaddadawa a wannan Alhamis cewa dole dakarun sojan Siriya su mutunta shirin tsagaita wuta a yankin Idlib da Turkiya da Rasha suka jagoranci tabbatar kafuwarta.

https://p.dw.com/p/3DPb3
Russland Iran Türkei Erdogan Putin Rohani Sotschi
Hoto: Reuters/S. Chirikov

A cewar Erdogan Turkiyya ba ta muradin karin ganin wani tashin hankali da al'umma ke shiga a yankin na Idlib da ke kusa da iyakar Turkiyya ko wani bangare na kasar ta Siriya. Erdogan ya bayyana haka ne a lokacin taron manema labarai da aka nuna ta kafar talabijin lokacin taron koli da ya halarta tare da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin da Hassan Rouhani na Iran a birnin Sochi da ke a kudancin Rasha.

Erdogan ya ce dukkanin shugabannin sun amince ba sa muradin ganin duk wani tashin hankali na sojoji bayan da Turkiyya ta kara daukar wasu matakai na musamman don ganin zaman lafiya ya samu a yankin. Ya ce sun kuma amince cewa shirin fitar dakarun Amirka daga Siriyar abu ne me kyau.