1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta kakkabe Kurdawa daga Afrin

Yusuf Bala Nayaya MNA
March 19, 2018

An daga tutocin kasar Turkiyya a yankin Afrin a ranar Lahadi bayan da dakarun kasar da 'yan tawaye da take mara masu baya sun kori sojojin tawaye na Kurdawa da suka mamayi birnin da ke Siriya.

https://p.dw.com/p/2uZ5y
Türkische Armee rückt in Afrin ein
Hoto: Reuters/K. Ashawi

A wani abin da ke zama babbar nasara ga mahukuntan na Ankara da dakarunsu suka dauki watanni biyu ana fafatawa da dakarun Kurdawa na YPG, dakarun kasar Turkiyya a karon farko sun kutsa kai yankin Afrin na kasar Siriya, ba tare da fuskantar wata babbar tirjiya ba inda suka dasa tutocin na Turkiyya a yankuna da dama na birnin.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kasar ta Siriya ta shiga shekara ta takwas ta yakin basasa, yayin kuma da aka shiga gumurzun fada mai zafi a birnin na Afrin da yankin gabashin Ghouta a kusa da birnin Damascus.

An dai halaka daruruwan mutane yayin da dubbai suka kaurace wa muhallansu.