1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Idlib: Siriya da Turkiyya na fafatawa

Mahmud Yaya Azare LMJ
February 12, 2020

Duk da ziyarar da tawagar Rasha ta kai kasar Turkiyya da nufin sabunta aiki da yarjejeniyar Astana da haifar da tsagaita wuta a yankin Idlib, har yanzu dakarun Turkiyya da na Siriya na ci gaba da yin artabu a Idlib din.

https://p.dw.com/p/3XfB4
Türkei l Präsident Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip ErdoganHoto: picture-allliance/AP/B. Ozbilici

Tun bayan kashe sojojin Turkiyya 13 a kan iyakokin da aka cimma tsagaita wuta tsakanin Turkiyyan da Rasha, mahkuntan Ankara suke ta tura dakarunsu zuwa yankin na Idlib da ya zama tungar karshe ga 'yan tawayen Siriyan. Dakarun na Turkiyya dai sun ce a hare-haren mayar da martanin da suka kai sun kashe sojojin Siriya masu yawa tare kuma da lalata manyan makamansu. Shugaban kasar Turkiyyan Recep Tayyip Erdoğan dai ya yi barazanar cewa hare-haren na somin tabi ne.

Kakkabo jirgin yakin Siriya

Mayakan 'yan tawayen da Turkiyyan ke goyon bayansu dai, sun yi ikirarin harbor wani jirgi mai saukar ungulu na dakarun sojin Siriyan, inda kafofin yada labarai ke ta nuna yadda jirgin ke fadowa a yayin da yake ci da wuta. Wani daga cikin 'yan tawayen dai ya ce illahirin wadanda ke cikin jirgin sun kone kurmus.

Syrien | Türkischer Militärkonvoi passiert Grenze
Tankokin yakin Turkiyya na jerin gwano zuwa yankin Idlib na SiriyaHoto: Getty Images/AFP/O. Haj Kadour

Hakan dai na wakana ne, a daidai lokacin da yayin da tawar  kasar Rasha har biyu da ke ziyara a Turkiyyan, ke barin kasar ba tare da an cimma wata matsaya a kokarin sabunta aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a arewacin kasar ta Siriya ba, lamarin da ya sanya wasu masharhanta ke nuna fargabar kara dagulewar lamura a yankin.

Rawar kasashen Rasha da Amirka

Tuni dai Amirka, wacca take goyan bayan wasu 'yan tawayen Kurdawa da ke rike da yankunan da arzikin man fetir din Siriyan ke kwance, ta jajantawa Turkiyya kan kashe sojojinta da aka yi tare da tura jakadanta na musamman zuwa birnin Ankara domin tattaunawa da mahukunta kan yadda za'a bullowa wannan sabon rikicin. Ga dukkan alamu kasar ta Turkiyya na cikin tsaka mai wuya a arewacin kasar ta Siriya, inda take kokarin kaucewa gwabzawa gaba da gaba da kasar Rasha da ke tallafawa dakarun Siriya wadanda ke kokarin mamaye yankin baki daya. A hannu guda kuma Ankaran da ta yi ammanar cewa duk da zakin bakin da Amirka ke mata a 'yan kwanakin nan, ba za ta lamunci Turkiyyan ta kafa sansanin tudun mun tsira a arewacin Siriyan ga miliyoyin 'yan gudun hijirar da ke kwarara zuwa kasarta a yankin ba.