1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a gabashin Ukiraine

Zainab Mohammed AbubakarDecember 30, 2015

Shugabannin kasashen Rasha da Ukraine da Faransa da kuma Jamus, sun amince da tsawaita yarjejeniyar sulhun Ukraine zuwa shekara ta 2016 mai kamawa.

https://p.dw.com/p/1HWKl
Petro Poroshenko Wladimir Putin Ukraine Russland Konflikt
Hoto: picture-alliance/dpa/Ch.Ena

A cewar wata sanarwar da ta fito daga fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin da ke bin diddigin tattaunawar shugabanin kasashen hudu ta wayar salula.

Tuni dai aka yi hasashen tsawaita yarjejeniyar, duba da yadda ake darajawa tsagaita wuta a yankin gabashin Ukraine tun daga watan Satumba, duk da cewar fada ya kan barke daga lokaci zuwa lokaci tsakanin 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha da dakarun gwamnatin Ukraine. A daya hannun kuma har yanzu ba'a aiwatar wasu batutuwa da aka cimma yarjejeniya a kansu ba.

A watan Febrairu ne dai aka cimma yerjejeniyar zaman lafiya a birnin Minsk din kasar Belarus, wanda zai fara aiki a karshen wannan shekara mai karewa, tare da bawa Ukraine 'yancin kulawa da garuruwan da ke kan iyakarta da Rasha.

Fadar gwamnati ta Kremlin ta ce shugabannin hudu sun jaddada bukatar darajawa yarjejeniyar tsagaita wutar, tare da goyon bayan tattaunawar kungiyar tuntuba ta Ukraine, da ke da nufin ganin an kafa doka da oda dangane da gudanar da zabe a yankunan da har yanzu ke hannun 'yan tawaye.