1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF: Yunwa ta kashe yara da dama a Borno

February 21, 2017

Bayan da Asusun kula da ilimin kanana yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar da wani rahoto da ke nuni da cewar akwai dubban yara da yaki ya raba da yankunansu da kefama da yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

https://p.dw.com/p/2Xyr4

Rahoto na UNICEF ya nunar da cewa daga cikin yara sama da miliyan daya da ake fargabar suna fuskantar barazanar mutuwa saboda yunwa da karancin abinci mai gina jiki akwai kimanin yara sama da dubu 400 a Najeriya. Wannan matsalar dai ta sanya asusun kula da ilimin kananan yaran na UNICEF ya bayyana cewa ya zama dole a dauki matakai na magance matsalar kafin a yi asarar wadannan yara. Wannan rahoto dai bai zo da mamaki ba ga yawancin masu aikin agaji da likitoci da ke aikin bada taimako a sansanonin 'yan gudun hijira a Maiduguri, inda suka ce lallai in ba a dauki matakin da ya dace ba alkaluman za su iya zarce hakan. Dr Sama'ila Idris wani jami'in kula da lafiya ne da ke aikin agaji a sansanonin 'yan gudun hijira na musamman wadanda ba na gwamnati ba a Maiduguri yana kuma daga cikin jami'an lafiyar da ke ganin tabbas akwai bukatar gaggauta daukar mataki.

Yunwa ta hallaka yara da dama a wasu kasashe da ke fama da rikici.
Yunwa ta hallaka yara da dama a wasu kasashe da ke fama da rikici.Hoto: Reuters/S. Modola

Akwai dai sauki wannan matsala ta yara masu fama da karancin abinci mai gina jiki a sansanonin da gwamnati da kungiyoyin agaji ke kula da su saboda yadda samar da abinci mai gina jiki da kuma magunguna dan magance cutuka. Sai dai a sansanoni wadanda al'umma ke kula da su lamarin ya yi kamari, wata kila saboda rashin mai da hankali a kansu inda sai likitoci kalilan ne ke ziyartar su don ba su kulawar da su ke bukata. A cewar Dr Hassan Maina Ali da ke zaman likita mai aikin bada agaji a sansanin 'yan gudun hijra da ake kira Fariya, tabbas halin da yaran ke ciki na yunwa abin dubawa ne. Domin magance wanna matsala ne ma kungiyar Likitoci na Gari na Kowa da ake kira da Medecins Sans Frontieres ko kuma Doctors Without Borders, ta bude wata cibiya mai gadaje 50 da ke kula da irin wadannan yara masu fama da yunwa da karancin abinci mai gina jiki. Yanzu haka ana bi ana zakulo irin wadannan yara da ke fama da yunwa a kuma mika su wannan cibiya da aka bude a yankin Fori da ke Maiduguri  domin kulawa da su. Amma a cewar Bashir Umar wani mai fafutukar kare hakkin yara wanda ke aikin agaji a sansanonin da ba na gwamnati ba, aikin ceto yaran ba na gwamnati ne kadai ba. Ya zuwa yanzu dai hukumomi a Najeriya ba su ce komai ba a kan wanan sabon rahoto, inda a baya suka bayyana cewa suna iya kokarinsu domin magance matsalar.