1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wa zai maye gurbin Paparoma?

February 12, 2013

Sa'o'i kalilan da bayyana aniyarsa ta ajiye mukamin sa na jagoran mabiya darikar Katholika a duniya, hankali ya fara karkata ya zuwa ga neman magaji ga Paparoma Benedick na 16.

https://p.dw.com/p/17cyp
GettyImages 161479608 This combo made with twelve file picture on February 11, 2013 shows Cardinals likely to succeed to Pope Benedict XVI who announced today he will step down at the end of this month after an eight-year pontificate. Top row from left : Brazilian Cardinal Claudio Hummes, Honduran Cardinal Oscar Andres Rodrigues Maradiaga, Argentine Archbishop Jorge Mario Bergoglio, Mexican Cardinal Norberto Rivera Carrera, Brazilian Joao Braz de Aviz, and Philippines' Luis Antonio Tagle. Bottom row from left : Austrian Cristoph Schonborn, Hungarian Peter Erdoe, Italian Angelo Scola, Canadian Marc Ouellet, Nigerian Francis Arinze, and Nigerian John Onaiyekan. AFP PHOTO (Photo credit should read DESK/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

Sannu a hankali dai hankali na karkata daga gabar tekun Mexico ya zuwa ga ita kanta Turai da ma kudancin Amurka da nufin neman magaji ga Paparoman wanda babu zato ba tsammani ya ce ya gaji kuma jikinsa na bukatar hutu.

To sai dai ita ma nahiyar Afirka ba a bar ta a baya ba a kokarin samar da shugabancin da ke zaman mafi girma da daukaka a tsakanin mabiya darikar Katholika sama da miliyan dubu daya a sassa daban daban na duniya.

Paparoma daga Afirka

Akalla mutane uku da suka hada da Kardinal Francis Arinze da Kardinal John Oniyekan sannan kuma da Kardinal Olabunmi Okogie ne dai yanzu haka ke iya hawa kujerar daga Najeriya kasar dake da mabiya miliyan kusan 20 banda kuma Kardinal Peter Turkson wani dan kasar Ghana da dukkaninsu ke iya zama Paparoma kowane lokaci a cikin watan Maris mai zuwa.

ARCHIV - Kardinal Peter Turkson, Präsident des Päpstlichen Rates für Gerechtigkeit und Frieden, spricht am 18.09.2012 in Frankfurt am Main mit einem Journalisten. Auch zwei Afrikaner sind immer mal wieder genannt worden, wenn es um die Nachfolge auf dem Stuhl Petri ging. Kardinal Peter Turkson aus Ghana ist so ein Kandidat. Foto: Frank Rumpenhorst/dpa (zu dpa 0647 "Nach Benedikts Überraschungscoup: Wer wird der nächste Papst?" am 11.02.2013) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Kardinal Peter Turkson na daga cikin wadanda ake ganin za su gaji Benedikt na 16Hoto: picture-alliance/dpa

Ana dai kallon zabar daya daga cikin hudun a matsayin kafa tarihin samar da baki na farko da zai shugabanci darikar mai tarihin kimanin shekaru dubu biyu.

Abun da kuma a cewar Reverend Father Zakaria Samjumi dake zaman daya daga cikin manyan jami'an kungiyar mabiya darikar a Najerya zai zamo abun farin ciki a garesu.

Wanene Francis Arinze

To sai dai koma wace ce hanya mafi bulla ga masu zaben sarki a cikin Vatikan din dai ya zuwa yanzu suna ambato Peter Turkson dan shekaru 64 kuma dan kasar Ghana da kuma Kardinal Francis Arinze dan shekaru 80 kuma dan Najeriyar da yayi suna a cikin fadar ta VatiKan a matsayin na kan gaba daga Afrika to sai dai shin wane ne Francis Arinze?

Reverend Father Ralph Madu dai na zaman sakataren kungiyar mabiya darikar Katholika a Najeriya mutumin kuma da ya fito daga karkara guda da Arinzen.

Kardinal Francis Arinze Galeriebild
Kardinal Francis Arinze ya shafe shekaru da yawa a fadar VatikanHoto: AP

“Na san Kardinal Arinze a matsayin mai wa'azi da kuma mai kula da makarantar wa'azi. Kuma na sanshi da dadewa na je ma bikin cika shekarunsa 80 a garin Onitsha. Mutum ne mai yawan addu'a kuma mai ilimi yayi aiki na shekaru da dama a Vatikan, saboda haka ya san diplomasiyar da aikin coci ba kawai a matsayinsa na shugaban hukumar hadin kan addinai ba har ma a matsayinsa na shugaban hukumar tabbatar da bauta da biyayya.”

Duk da cewar dai bullar daya daga cikin biyun ba zai zamo Paparoma na farko daga nahiyar ta Afirka ba, dukkanin ragowar Paparoma ukun da suka fito daga nahiyar dai fararen fata ne kuma Romawa ga cocin da yanzu haka ruhin ta ke zaman dagewa irin ta mabiyan nahiyar.

Infografik Katholiken in der Welt HAU DW-Grafik Peter Steinmetz/Olof Pock 13.02.2013
Yawan mabiya dairkar Katholika a sassan duniya daban daban

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani