1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wa'adin da aka bai wa Kataloniya ya cika

Ahmed Salisu
October 19, 2017

A wannan Alhamis din ce wa'adin da hukumomin kasar Spain suka bai wa na yankin Kataloniya kan su yi watsi da batun ballewa daga kasar ko kuma ballewar ke cika.

https://p.dw.com/p/2m933
Spanien Carles Puigdemont bei einer Demonstration in Amer
Shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemont yyin wata zanga-zangaHoto: picture-alliance/dpa/R. Townsend

Tuni gwamnatin ta Spain ta sha alwashin soke cin gashin kan da ta bai wa yankin na Kataloniya idan har ya ki cin tuwon fashi wajen ayyana samun mulkin kan yankin. Shugaban na Yankin Kataloniya Carles Puigdemont, na da wa'adin harya zuwa karfe 10 na safiya na ya bai wa hukumomin na Madrid amsa. Sai dai kuma idan har ba su yi hakan ba to gwamnatin ta Spain da Firaminista Mariano Rajoy ke jagoranta za ta yi amfani da kudiri mai lamba 155 na kundin tsarin mulkin kasar ta Spain da ke bada damar soke wani bangare ko kuma gabaki dayan cin gashin kan da yankin na Kataloniya yake tinkaho da shi.