1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wa´adin shugabancin wata 6 da Jamus ta yiwa ƙungiyar EU ya kare

June 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuHU
Jamus ta kawo karshen wa´adin shugabancin wata 6 da ta yiwa KTT EU kuma ta mikawa kasar Portugal ragamar mulkin kungiyar har izuwa karshen wannan shekara. Dazun nan aka yi bukin mika mulkin a birnin Berlin tsakanin ministan harkokin wajen Jamus F.-W. Steinmeier da takwaransa na Portugal Luis Amado. Ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner ya mika godiyar kasar sa ta musamman ga Jamus bisa shugabanci da ayyuka na gari da ta yiwa kungiyar EU a wa´adin shugabancin ta na watanni 6. A lokacin shugabancin ta Jamus ta shawo kan EU ta amince ta rage kashi 20 cikin 100 na hayakin dake dumama doron kasa kafin shekara ta 2020 kana kuma ta share fagen cimma sabuwar yarjejeniya da zata sabunta ayyukan kungiyar mai kasashe membobi 27.