1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayar da 'yan gudun hijrar Afirka gida

Usman Shehu Usman
May 13, 2022

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi kan kuri'ar kara wa'adin zaman sojojin Jamus a kasar Mali.

https://p.dw.com/p/4BHCY
Mali | Militär | FAMA | Armed forces
Sojojin MaliHoto: Souleymane Ag Anara/AFP

Ba wai kara wa'adin ne ya fi daukar hankali ba, hasali ma shi ne dai kasar ta Jamus ta sanar da kara yawan dakarunta a Mali.

Bayan majalisar zartarwa da ta dokoki suka amince da kara tsawaita zaman sojojin na Jamus a kasar Mali, sun kuma kara cewa za a tura karin sojoji har 300 izuwa Mali. Abin da ya dauki hankali kuwa shi ne a makon bayan nan ne aka sanar cewa kasar Jamus ta sanar da janye sojojinta daga Mali izuwa kasar Nijar.

Don haka abinda ake bukatar sani a nan shi ne wadannan sojojin za su je ne don yin aiki karkashin rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD da ke a kasar Mali wacce aka sani da MINUSMA, kuma ana ganin cewar karin sojojin na Jamus za su je ne don maye gurbin sojojin Faransa da aka janye daga rundunar bayan samun baraka tsakanin Mali da Faransa.

Außenministerin Baerbock besucht Mali
Sojojin Jamus da ke MaliHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Sai jaridar die Welt wacce ta sake duba batun mayar da 'yan gudun hijiran Afirka daga London zuwa Kigali. Jaridar ta ce gomma a Ruwanda maimakon a Birtaniya. Wato dai tsari ne da gwamnatin Birtaniya ta kulla na kwashe 'yan Afirka da ke kasarta suna jiran samun mafakar siyasa, don haka ta gwammace ta biya ta kudi wa kasar Ruwanda, don tsugunar mata bakin daga Afirka.

Die Tageszeitung ita kuwa ta yi sharhinta ne kan rikicin da yankin na gabashin Afirka ke fama da shi.  Jaridar ta ce tashin hankali daga Kwango har izuwa Mozambik duk yankin na gabashin Afirka na fama da yaki. Misali dai shi ne wargajewar tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da 'yan tawayen kasar, wanda bayan tattaunawar ta wargaje hakan ya bude sabon yaki tsakaninsu. Yayin da wannan ke faruwa can a ana yaki da kungiyoyin da ke ikirarin yin jihadi, wanda yanzu haka Yuganda ke yaki da wasunsu cikin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango yayin da ita kuwa kasar Ruwanda ke yaki da wasu 'yan jiadin a kasar Mozambik.

Impfkampagne in Südafrika
Allurar rigakafin corona a Afirka ta KuduHoto: Siphiwe Sibeko/AP Photo/picture alliance

Sai dai jaridar Neue Zürcher Zeitung, wacce ta duba batun alluaran riga kafin corona. Jaridar na mai cewa yanzu alluran nan amma kuma ba masu bukatar saya. Fara sarrafa magungunan a kasar Afirka ta Kudu na da nufin sa kasashen Afirka su daina dogaro da kasashen yamma wajen samun riga kafin na corona, amma kuma da alama ba mai yiwuwa ba ne.