1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Waiwaye kan manufar Yar'adua

May 6, 2010

Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar'adua ya bayyana tsare tsaren ci gaban ƙasar da mulkin gwamnatinsa take son aiwatar

https://p.dw.com/p/NFld
Umaru Yar'AduaHoto: AP

Kamar dai yadda aka sani a daren jiya ne Allah ya yiwa shugaban Najeriya Alhaji Umaru Musa Yar'adua rasuwa, bayan doguwar jinyar da ya yi fama da ita.

Ya 'yan uwana 'yan Najeriya, ina mai farin cikin cewa kun zaɓe mu ni da mataimakina Goodluck Jonathan, domin mu gina wani sabon ƙarni na ƙasa ɗaya mai kula da al'ummarta"

Alhaji Umaru Musa Yar'adua wanda ya karɓi shugabancin ƙasar bayan shekaru takwas yana gwamnan Jahar sa ta Katsina, ya bayyana fatar sa ga 'yan ƙasar a wani hirar da ya yi da gidan radiyon Deusche Welle.

"Na farko dai mu zai da gaskiya, mu yi aiki tuƙuru mu bar lalaci da rashin gaskiya da cin hanci. Duk irin waɗan nan halayen mu kau da su cikin ayyukanmu, wannan shine abinda za mu yi a gwamnatin mu"

To sai dai wani ƙalubalen da gwamnatin Alhaji Umaru Musa Yar'duwa ta zo ta tarar shine batun yankin Naija Delta. Matsalar da kuma za'a iya tunawa da gwamnatinsa kenan, domin Yar'aduwa ya samu nassarar shawo kan wannan matsalar.

"Magance Matsalar yankin Naija Delta yana buƙatar matakai daki daki. Don haka muka samu nassar kafa wani tsari wanda zai samu karɓuwa daga baggarori daban daban. Bayan mun samu wannan haɗin kai to sai mu tinkari batun warware matsalar 'yan bindiga daɗi dake tada zauna tsaye a yankin"

Tun ranar rantsuwarsa a matsayin shugaban ƙasa a gaban dubban 'yan ƙasar da baƙi waɗan da suka hallarta, Yar'aduwa ya fito da bakinsa yace zaɓen da akayi masa yana cike da kura kurai, amma dai zai tabbatar da yin ƙyara, wanda zai inganta zaɓen ƙasar.

"Zan kafa kwamiti wanda zai duba dukkan zaɓuɓbukan da suka gabata a Najeriya, yadda akeyinsu yadda ake tafiyar da su, da yadda ake tafiyar da aikin zaɓen, da yadda dokoki waɗanda da su ake bi a lokacin zaɓe, ta yadda zamu gyara zaɓen, za mu duba mi yake hana zaɓen ƙasar mu baya inganci kamar na sauran ƙasashen duniya"

A ƙarshe dai Alhaji Umaru Musa Yar'adua ya yi wata ƙira ta musamman ga 'yan Najeriya, don su ɗau matakai waɗan da na baya zasu tuna da su.

'Yan uwana 'yan Najeriya ina kira garemu, da lokaci ya yi duk abin da za mu yi mu   yi aiki tuƙuru mu bar son zuciya. Mu tsaya mu gina ƙasarmu, mu gina wani tushe wanda zamu ji daɗin rayuwa wanda na bayanmu zazu zo suyi ra yuwa mai inganci" 

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammad Nasiru Auwal

Kuna iya sauraron rohoto da Muryar Yar'adua a ƙasa