1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wanene William Rodriguez

January 9, 2008

Taƙaitaccen tarihin William Rodriguez

https://p.dw.com/p/Cn65
Cibiyar Kasuwanci ta DuniyaHoto: AP

Masu saurarommu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Tambaya: Ku bani tarihin William Rodriguez, kuma wai shin ko shi ne Mutum na ƙarshe da ya tsira daga harin 11, ga watan Satumba da aka kai kan tagwayen ginin nan na birnin Newyork dake Ƙasar Amirka ? Wannan ita ce tambayar da Abdul’aziz Dan’azumi daga Bauchi a Najeriya ya aiko mana.

Amsa: To Mallam Abdu’ aziz, shi dai William Rodriguez, bincike ya nunar da cewa shi ɗan asalin yankin Puerto Rico ne, inda ya yi ƙaura zuwa birnin Newyork ta ƙasar Amirka.

Lokacin da ya je Newyork, ya fara aiki a matsayin ƙaramin ma’aikaci a babbar cibiyar kasuwanci ta newyork, inda da farko ya soma a matsayin mai sharar ofishin gwamna Cuomo, har ya kai ga wani lokaci ma shi ne yake shirya wa Cuomo taron manema labarai.

Bayan da gwamna Cuomo ya bar ofishin, daga baya an komar da Rodriguez zuwa aikin share matakalar hawa benen na world trade center, wato babbar cibiyar kasuwancin ta birnin newyork , inda aka tura shi ya riƙa share ɓangaren arewaci na ginin, wanda da haka ne har ya kai matsayin babban jami’i mai riƙe da “Master key” wato makulli guda ɗaya da yake buɗe kowacce ƙofa ta wannan gini. Rodriguez yana nan bakin aiki a lokacin da aka kai wasu hare-hare na farko tun cikin shekara ta 1993, kafin wanda aka kai na baya bayan nan a shekara ta 2001. A takaice ya shafe shekaru kusan 20, yana aiki a wannan cibiya ta kasuwanci dake Newyork.

William Rodriguez, kan kasance ne a bakin aiki da ƙarfe 8.00 am to amma yayin da yake amsa tambayoyi da aka yi da shi ta gidan Talabijin na CNN, Rodriguez yace a ranar 9 ga watan Nuwamba, ranar da aka kai harin, bai je ofis kan kari ba, ya makara da misalin mintoci 30, don haka a lokacin da ya shigo ginin bayan an sami ɗan lokaci sai ya ji karar wani abu mai kamar fashewa a cikin ginin, yayin da ya je don duba ko menene ya faru sai ya kuma jin wata ƙarar fashewar, to amma yadda ginin ya girgiza da farko, a lokacin ne Jirgin farko ya afka cikinsa, to sai dai kuma ya zaci cewar Injin Jannareto ne ya fashe, bai zaci cewar Jirgi ne ya kutsa cikin ginin ba.

To misalin ƙarfe takwas da minti 46, Rodriguez ya yi ƙoƙarin neman gane ko me ke faruwa, don haka sai ya je ga wani mai kula da ginin, suna cikin tattaunawa sai ga wata fashewar daga sama inda har ya kai ga tsattsagewar ginin, sannan sai rufin cikin dakin da suke ya soma rusowa. To ana cikin haka can sai ga wani ya dumfaro gaban na’urar jigilar mutane ta bene, wato elavator, da munanan raunuka a jikinsa , suna cikin haka sai kawai suka fara hango manya-manyan ɓarɓashin wuta suna ruguzowa daga saman benen suna afkawa ga sassan bene, inda nan take tagogi, da kuma na’urorin jigilar suka soma kamawa da wuta, duk inda ka duba sai ka ga jama’a kowa na ta kansa.

William ya ce “nan take sai na soma taimakawa mutumin nan na farko da ya iso wurin da nake tattare da raunuka daban-daban jikinsa, na fitar da shi da hanzari na sama masa motar daukan marasa lafiya , sannan na komo na ci gaba da taimakawa waɗanda wannan tashin hankali ya ritsa da su a benen”. Saboda da irin wannan agaji da William Rodriguez ya bayar, har ya sami wata lambar karramawa ta Ƙasa ta seanata Puerto Rico.

Rodriguez shi ne Mutum na ƙarshe da ya bayar da bahasi gaban hukumar binicken hare-haren na newyork. Sanadin hare-haren ne ma ya sa ya yi fice, jama’a ta san da zamansa wanda har ya sami shiga cikin ayarin mambobin hukumar agaji ta daraktocin 911. Koda yake dai akwai Mutane da suka kai dubu 1,200 da suka ba da bahasi gaban wannan hukuma a bainar jama a, to amma shi Rodriguez, ba a yarda ya ba da nasa bahasin gaban jama’a ba, dukkan abin da ya fadi lokacin da ake yi masa tambayoyi, ba a hada da su ba a ƙunshe cikin rahoton hukumar. To wannan abu ya yi matukar ɓata masa rai, don kuwa ya gaya wa hukumar binciken tare kuma da hukumar binciken sirri ta FBI cewar, waɗanda suka kai hare-haren, shi da kansa ya gansu a harabar cibiyar kasuwancin ta newyork, yan watanni kafin a kai hare-haren, kuma ya haƙƙaƙe cewar zai iya gane mutumin da ya shugabanci abin.

Domin nuna damuwarsa ne kan wannan lamari William Rodriguez, ya shigar da ƙara, inda cikin ƙarar ya ƙalubalanci manya -manyan masu faɗa aji na Amirka sakamakon yadda aka ɓoye irin bayanan da ya bayar na game da wannan hari na ranar 11,ga watan Satumba. Cikin waɗanda Rodriguez ya ƙalubalanta harda Geroge W. Bush, da Richard Cheney, da Geroge T. Tenet, da Tom Ridge, da Condoleezza Rice, da Paul Wolfowitz, da Richard Myers, da hukumar bada agajin gaggawa ta Amirka, da hukumar tsaron cikin gida ta Amirka da dai sauransu. Baki ɗaya akwai Mutane 156, da lauyansa ya shigar da Ƙararsu a kotun gundumar gabashin Pennsylvania, inda ya ƙalubalance su kan cewar waɗanda ake zargi da hannu wajen shirya hare-haren, ba sune suka kai su ba.Domin shi Mutanen da ya gani ba Larabawa ba ne. Kuma babu wani mai sunan Larabci a cikinsu.

Cikin watan Disamba na 2004, gwamnatin Amirka ta gabatar da wani ƙudiri don yin fatali da wannan ƙara da Rodriguez ya shigar, kan dalilan da gwamantin ta bayyana na rashin sahihancinsa, tare da hujjar cewa an shigar da ƙarar a kotun da ba ta dace ba.

Don haka ne a ranar 17, ga watan Yuli na shekarar 2006, kotu ta yi na’am da wannan bukata ta gwamnati, inda ta yi fatali da ƙarar nan take.To wannan al’amari ya ɓata wa Rodriguez rai, har ya kai ga bayyana gaskiyar lamarin abin da ya faru game da hare-haren 11, ga watan Satumbar ga dukkanin kafofin da ya san zai iya tuntuɓa.

Dangane da tambayarka Abdul-Aziz na cewar, wai ko shin gaskiya ne Rodriguez ya musulunta? E gaskiya ne. Kuma za a

iya samun cikkakun bayanai ne daga American free Press, lamba 645, Pennsylvania Avenue, SE, Suite 100, Washington, D.C 2003. Kuma domin samun cikkanen bayanin komai da komai, za a iya tuntuɓar shafin yanar gizo na shi kansa William Rodruguez akan adireshi kamar haka (www.911keymaster.com).